ALAMOMIN SIHIRIN HANA HAIHUWA
*ALAMOMIN SIHIRIN HANA HAIHUWA* ========================== Bismillah, wassalatu wassalamu ala Rasulillah. Yadda za ka gane an yi ma sihirin hana haihuwa ___________________________________ Ta 6angaren namiji:- 1-rashin sha‘awa sam-sam. 2-‘kin mikewar gaba sanda kai nufin yin jima‘i. 3-‘kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana iya zama a cikin marainan mutum. 4-saurin gajiya, yayin jima‘i. 5-jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in haihuwa yayin jima‘i. 6-rashin cimma bukatar jima,i. 7- in ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka. 8- da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo tun kafin ka fara. 9- komawar gaba da maraina su shige ciki. 10- yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili, faduwar gaba, da dai sauran su. 11- haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka. Ta 6angaren mace; 1- yawan ciwon ciki mai tsanani da yin jiri. 2- a duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta ga jini ya zo ma ta. 3...