MATSALOLIN MATA
MATSALOLIN LOKACIN AL'ADA
*********************************
Mata da Yawa Su kan fuskanci matasaloli daban daban a lokacin da al'adarsu ta zo. Wasu kanyi fama da lalurar zubar jini da fitar wasu farin ruwa mai yauki da kuma wari.
Ciwon mara a lokacin alada kan farune a lokacin da mahaifa ke curewa da motsawa waje guda domin fitar da wani abu daga cikinta marar amfani wanda wannan motsin shike saka wannan ciwon na mara.
Akwai abubuwa dakan-daban da ke zuba daga alaurar mata alokacin wannan ciwon kamar jini ko mai hade da ruwa ruwa, farin ruwa, ruwa mai kauri, ruwa mai
wata kala daban, da sauransu.
Irin wannan kan farune saboda shigar wata matsala ta kwayoyin cuta a lokacin Al'adar, kamar, Virus, yeast infection, shan kwayoyin hana daukar ciki, Saduwa barkatai, Ciwon suga, cancer, da sauransu.
Wani lokaci alada kan rikice ko
tsallake ba tare da tazo ba kuma ba tare da shigar cikiba.
Zubar jinin haila kowace mace nada nata mataki daban daban wanda kan auku kafin saukar jinin a kowane wata. Wannan jini kan sauko ne daga mahaifa wanda kuma dazarar ya dauke anfi daukar ciki musammam kwamaki hudu ko biyar na farko.
Zaifi kyau a lura da zuwan lokacin
alada da adadin yawan jinin da yawan kwanakin daya dace wadda idan har yayi nisa shine kwana
shida amma ga yan mata yara baya wuce kwana daya zuwa biyu.
Idan ana fama da ciwo alokacin alada ko lokacin karatowar alada, ko fama da ciwon mara, ko rashin walwala a lokacin Al'ada, ko Rashin kin cin abinci, ko yawan kasala, ko nauyin jiki, ko yawan tashin Zuciya a lokacin Al'ada, akwai matakan da ake bi domin samun saukin wayannan matsalar alokacin Al'ada. Ga matakan kamar haka;
1. Sanin alamomin zuwan jinin kafin ya sauka, hakan kan temaka wajen tsara alamuran yau da
kullum da ragewa kai wahala da kuma samun nishadi, motsa jiki dacin abu marar nauyi.
2. Lura da abubuwan da ake ci lokacin alada ko karatowarta, da rage cin gishiri don yana tara ruwa ya kuma hana jinin fita idan yayi yawa sai jiki yafara nauyi da kumburi.
A kuma guji cin soyayyun abubuwa da gyada, yaji, kayan fulawa, a guji shan naskofi, da lemon kwalba, goro. Da sauransu. Wayannan abubuwa cin su ko shansu a lokacin da al'ada tayi kusa suna rikita lokacin alada. A rika yawaita
cin 'ya'yan itatuwa, don suna rage ciwon na mara.
3. A rage shan magunguna barkatai. Musamman wayanda ba'asan in gancidu ba.
4. A rika shan 'ya'yan itatuwan da ke kara jini idan haila ta yawaita.
5. Idan mara ko ciki na ciwo sosai, za'a iya kwantawa waje daya ta hanyar jingino da matashi
da kuma yin numfashi kamar ana hakki. Wannan zai taimaka ya saukar da ciwon.
6. Haka ma idan mara na Ciwo za'a iya jika tawul da ruwan zafi ko sanyi a dora a saman mara ko goshi, hakan kan kawo sassaucin ciwon.
7. Idan mara na Ciwo za'a iya jika Tsamiya idan ta jiku a tace a Zuba Man Zaitun Wannan yana saurin warkar da Ciwon Na Mara musamman a lokacin Al'ada.
DAGA BIRNIN MAGAJI ISLAMIC CENTER RIJIYAR ZAKI KANO
08080678100
KADAN DAGA DALILAN DAKE JAWO RASHIN ZUWAN JININ AL'DA
◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆
1*DAUKAR CIKI
2*SHAYAR WA
3*SHIGA KUNCI KO DAMUWA
4*YIN AIKI MAI WAHALAR GASKE
5*SHIGA ACIKIN TSORO MAI TSANANI
HANYAR MAGANCE YAWAN ZUBAR JININ AL'ADA(MENORRHAGIA)
◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆
◆Ganyen garafuni
◆sabara
◆Ganyen marke
Ayi garinsu adingasha a tea 21days
RASHIN ZUWAN JINI ALOKACINSA
◆◆◆◆◆◆◇◆◆◇◇◇◆◆◆◆◆◆◆◆◆
◆RIDI
◆JAN ALGARIF
◆MAN RIDI
Ahada azuma mekyau cokali uku arana kwana 9
Affectin d femal system
◆Ciwon mara b4 al'ada
◆Kwarar jini fiyeda kima
◆Komarsa bayan tsayawarsa
◆rashin zuwa'al'ada asadda yakamata
MINSHARI ACIKIN BACCI
◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆◆
indai zaka zuba man zaitun acikin shayinka kullum sau 2 arana kwana 8 tozakayi bankwana da minshari
Indai zakasha shayin zallar babunaj kwana goma ajere tareda zuma kadena minshari kenan
Comments
Post a Comment