SHAWARA GAMASU NEMAN HAIHUWA
*SHAWARA GA MASU NEMAN HAIHUWA*
🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻🤰🏻
Da farko dai ya kamata ma’aurata su san cewa akwai abubuwa da dama da kan iya shafar lafiyar zamantakewa a bangaren samun haihuwa. Wadannan abubuwa sun hada da shekarun ma’auratan da lafiyarsu da kuma ilminsu. Miji da mata, kowanne zai iya zama shi ne sanadin rashin haihuwa, ba mace kadai ba kamar yadda aka fi alakantawa a al’adance.
A bangaren shekaru, macen da ba ta wuce shekaru 25 ba ta fi saurin samun iri, fiye da wadda ta gota. Yawancinsu (kashi 90 cikin dari), cikin wata shida na aure suke samun juna biyu. Wadda ta haura 35 sai an dan sha wahala domin kwayayenta na raguwa ne daga wadannan shekaru. Shi ma namijin da ya haura shekaru hamsin, kwayayensa na kasa sosai. Amare masu son samun juna biyu da sauri, kamata ya yi da sun shiga gidan miji su fara shan kwayoyin magunguna na bitaman da folic acid domin taimakawa kwayayensu
A bangaren lafiya masu cututtukan suga ko hawan jini ko ciwon sanyi ko na damuwa, namiji ne ko mace, su san cewa su ma a lokuta da dama sukan dade kafin su samu rabo. Yawan aiki ba hutawa da taba sigari da barasa duk sukan lalata kwayayen mace da na namiji, haka ma kiba. kwayoyi ko allurar hutun haihuwa ma za su iya kawo jinkirin samun juna biyu ko da an bar shan su.
Ta bangaren ilmin zaman aure kuma dole mace ta san cewa akwai ranakun da ko mai gidanta ya kusance ta ba za a samu komi ba, akwai kuma ranakun kuma da akan yi dace. Ya kamata mace ta san cewa ranaku goma zuwa sha biyar bayan al’ada su ne ranakun da ba kwai a mararta, kuma da wuya a samu juna biyu, ranaku goma zuwa sha biyar kafin wata al’adar su ne na kyautata zaton samun rabo. Daga lokacin da mace ta saki kwai a mararta zuwa fitowarsa cikin mahaifa, da yin jinin al’ada kwana biyu ne zuwa uku kacal. A daidai wannan lokaci kuma idan mace ta auna dumin jikinta da na’urar thermometer, za ta ga ya dan yi sama kadan, idan ita mai amfani da wannan dabara ta sanin ranakun fitowar kwayayenta ce ke nan. Shi kuma kwan namiji yakan iya kwanaki hudu ko ma biyar a mahaifar mace yana jiran kwan nata. Ke nan kwanaki biyar zuwa bakwai na dab da al’ada su ne aka fi alakantawa da sa’ar samun juna biyu. Yawan tafiye-tafiyen mai gida ke nan kan sa irin wadannan ranaku su subuce.
DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP
☎08080678100
Comments
Post a Comment