ALAMOMIN SIHIRIN HANA HAIHUWA
*ALAMOMIN SIHIRIN HANA HAIHUWA*
==========================
Bismillah, wassalatu wassalamu ala Rasulillah.
Yadda za ka gane an yi ma sihirin hana haihuwa
___________________________________
Ta 6angaren namiji:-
1-rashin sha‘awa sam-sam.
2-‘kin mikewar gaba sanda kai nufin yin jima‘i.
3-‘kin fitowar ruwa yayin jima‘i, domin Aljanin yana
iya zama a cikin marainan mutum.
4-saurin gajiya, yayin jima‘i.
5-jin motsi kamar tafiyar wani abu a ga6o6in
haihuwa yayin jima‘i.
6-rashin cimma bukatar jima,i.
7- in ka yi nufin yin jima‘i sai bacci ya dauke ka.
8- da ka yi niyyar yin jima‘i kawai sai ka ji ka kawo
tun kafin ka fara.
9- komawar gaba da maraina su shige ciki.
10- yawan ciwon kai, 6acin rai mara dalili, faduwar
gaba, da dai sauran su.
11- haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka.
Ta 6angaren mace;
1- yawan ciwon ciki mai tsanani da yin jiri.
2- a duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta
ga jini ya zo ma ta.
3- jin zafi yayin jima‘i da rashin samun wata fa‘ida.
4- suna gama jima‘i sai maniyyin da mijinta ya zuba
ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta
ba.
5- matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.
6-‘kin yarda da jima‘i.
7-yawan mafarkin wani na saduwa da ita.
8- yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da
taron suna.
9- ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa
a cikin ta ya fizgo wani abu.
10- yawan yin 6arin ciki ba tare da wani sanannen
dalili ba.
11- yawan mafarkin ana bin ki a guje ko ana
kokawa da ke.
12- jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma ar yana
dada girma, amma in likitoci suka auna za su ce ba
su ga komai ba.
13- rashin son yin magana da kowa da jin haushin
mutane.
14- tsanar mai gida haka kawai.
15- yin doyin farji da ‘kai‘kayin gaba da ‘kurajen
gaba.
Da dai sauran su.
Mafita shi ne ka ziyarci mai Rukiyya don ya dora
ka akan tsarin maganin da ya dace da kai.
Kuma ka dinga zama da alwala da addu‘o‘in safiya
da maraice.
Amma dai sihiri da Aljani ba su isa su cutar da kai
ba sai da iznin ALLAH.
DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP
akarkashin jagorancin
*BIRNIN MAGAJI ISLAMIC MEDICINE CENTER RIJIYAR ZAKI KANO*
☎08080678100
Comments
Post a Comment