*AMFANIN RAKE GA MATA MASU CIKI
Da yawan mata da ke dauke da juna biyu na yawan tambayar ko akwai wani amfani a tattare da shan rake yayin da ciki ya fara tsufa? Shin ko babu matsala mace mai juna biyu ta ke shan rake? Ko shan rake na taimakon jaririn dake ciki ko ya yi ma sa wata illa?. Amsar masana lafiya a kan wadannan tambayoyi sun kasu gida biyu; amfani da kuma illar shan rake yayin juna biyu. Amfanin rake ga mace mai juna biyu: A yayin da mace ke da juna biyu, duk abinda ta ci ko ta sha na da tasiri ga lafiyar dan da ke cikin mahaifar ta. Sanannen abu ne cewar yawan cin 'ya'yan itace da tasiri wajen inganta lafiyar dan da ke cikin mahaifa. Rake dan itace ne da ke da ruwa mai zaki. Rake na dauke da sinadarin protein da ke taimakon kwayoyin halittar jikin dan adam. Mata ma su ciki kan fuskanci taurin bahaya. A cikin ruwan rake akwai sinadaran da ke sa ka bahaya laushi, bisa wannan dalili, masana sun bayyana cewar shan rake na da kyau ga ma su juna biyu. Amfani da illolin rake ga Mata ma su ju...