ILLOLIN CIWON SANYI GA Y'AY'A MATA
*MATA MASU FAMA DA SANYI,YADDA ZAKI MAGANCE SHI CIKIN SAUKI*
👙👙👙👙👙👙👙👙👙
Sanyin Mata sanyi ne wanda ke shafar baakin mahaifa,wani bangare na mahaifar ko mahaifar gabadayanta.
Sanyi Yana da matukar illa,yakan iya janyo miki kansar bakin mahaifa ko ma yahanaki haihuwa Baki daya.
Wannan matsalar dai amfi samunta ne a matanmu na Nan Africa.
Bincike yanuna cewa sanyi shine Abu NAFARKO Wanda yake kawo Rashin haihuwa acikin al'ummarmu.
*MATAN DA ZASU IYA KAMUWA DA DASHI*
Matan da Kan iya kamuwa sunkunshi:
1.matan da basa kula da tsaftar jikinsu
2.matan dake saduwa da namiji sama da daya
3.wadanda ke saduwa da namijin da yake da abokan tarayya sama da daya.
4.Mace Yar kasa da shekara 25 datake yawan saduwa da Maza dayawa
5.Matar dake yawan wanke gabanta daga ciki da ruwa ko kayayyakin mata
6.Matar da take amfani da maganin kayyade iyali Wanda ake sakawa a cikin mahaifa(watoh iucd).
7.Matar da tataba fama da wannan ciwo ada.Duk wadannan matan kan iya kamuwa dashi.
*YADDA ZAKI GANE KO KINA DAUKE DASHI*
Alamomin wannan cuta dai sun hada da:
1.ciwon Mara
2.kaikayin gaba
3.fitar ruwa tagaba wani sa'in Mai wari
4.ciwon Kai
5.zazzabi
6.al'ada Mai Wasa ko
7.ganin jini yayin saduwa ko bayan hakan
jin ciwo ko zafi alokacin saduwa
8.yawan fitsari ko Shan wahala yayin fitsari.
Duk Matar dake da wandannan alamomi toh bamakawa Tana da sanyi a jikinta.
*ILLOLIN DA ZAI IYA JANYO MIKI INBAKI MAGANCE SHIBA*
1.Hana haihuwa(rashin haihuwa)
Cutar sanyi Kan iya Hana haihuwa agaba,musamman idan mutun yadade Yana fama dashi batare da daukar wani mataki ba.
2.lalata mahaifa
Sanyi Yana iya lalata mahaifa ta hanyar yimata tabo sosai(synechiae)ko yajanyo toshewar hannun mahaifa(tubal blockage).
3.Kansar bakin mahaifa
Shin menene gaskiar cewar akwai alakar sanyi da kansar mahaifa?ko mace Mai sanyi zata iya kamuwa da kansa?
Eh a hakikanin gaskia mace Mai sanyi tanada yiwuwar kamuwa da kansar bakin mahaifa da mahaifa.
4.Hana daukar ciki
Mace Mai sanyi zata iya daukar ciki Amma wannan abune mai wahala musamman idan ta dade Tana fama da wannan cuta.hakan nafaruwa ne sabida tabon da sanyin ke yiwa mahaifa.
5.Daukar ciki awajen mahaifa
Mace Mai sanyi nada yiwuwar samun ciki Wanda ba acikin mahaifa mazuguninsa yake ba(watoh ectopic pregnancy).
*ABUNDAA YAKAMATA KIYI*
Yana da kyau duk matar da take da alamomin damuka lissafo datayi gaggawar ganin likita domin gujewa matsalolin da zata iya gamuwa dashi agaba Kamar na Rashin haihuwa.
Yazamanto abokin saduwanta Shima anyimasa gwaji tare da ita,an tabbatar shima bashi da ita,Rashin yin hakan Kan iya sa sanyin ya Kara dawowa agaba Koda kuwa tawarke.
Gwajin da Ake bayarwa sunkunshi:
1.High vaginal swab
Wannan gwajin shi zai nuna wane magani yafi cancanta abaki, rashin yinsa kan iyasa kin dace wa wajen maganin sanyin.
2.Hotan ciki
3.Gwajin jini
4.Gwajin fitsari
Daganan sai ayi kokari anemi sahihin maganinda zaitaimaka wajen kawarda wannan cuta mai lahani ga y'ay'a mata harma da maza,amma anemi maganin awajen kawararrun masana dan kaucewa sake jawo wata matsalar,kokuma atuntubemu a mazaunin mu dake garin kano kantitin rijiyar zaki.
*DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP*
☎️08080678100
Comments
Post a Comment