AYYUKAN HANTA
Allah Gwani | Ko Ka San Ayyukan Hanta A Jikin Ɗan Adam?
1. Hanta guda ce daga cikin muhimman kayan ciki. Kuma tana nan a cikin ciki a ɓangaren dama daga sama, ƙasa da faffaɗar tsokar nan da ta shingice tsakanin ciki da ƙirji.
2. Nauyin hantar mutum ya kai nauyin kilogiram ɗaya da rabi (1.5kg).
3. Hanta na samun jini da ya kai yawan lita ɗaya da rabi (1.5L) a kowane minti ɗaya.
4. A hanta ne ake gama narka sinadaran abinci yadda jiki zai iya amfani da su kamar dangogin siga, furotin, kitse/mai, magunguna, bitamin da sauransu.
5. Hanta taska ce da ke ajiye muhimman sinadarai zuwa lokacin da jiki zai buƙace su, kamar siga, narkakken furotin, nau'o'in bitamin da sauransu.
6. Hanta na samar da sinadarai kamar gulokos, narkakken furotin da sauran muhimman sinadaran da jiki ke buƙata.
7. Hanta ce ke samar da ruwan maɗaciya. Ruwan maɗaciya na amfani wajen narka abinci ajin kitse/mai yadda jiki zai iya zuƙar kitse/mai daga ƙaramin hanji zuwa cikin jini sannan jini ya kai shi zuwa dukan sassan jiki.
8. Hanta na yin aikin kawar da guba, muggan sinadarai da ƙwayoyin cuta kamar bakteriya da bairos.
9. Hanta na sarrafa / samar da jini ga ɗan-tayi, haka nan, tana ajiyewa da samar da muhimman kayayyakin sarrafa jini kamar sinadaran 'vitamin B12' da 'Iron'.
10. Jajayen ƙwayoyin jini na shafe kwanaki 120 suna rayuwa ne a jiki. Bayan saifa, hanta na daga cikin sashin jiki da ke kashe raunanan jajayen ƙwayoyin jini bayan sun cika kwanaki 120 suna aiki.
11. Hanta ce sashin da ke samar da mafi yawan zafi/ɗumi da jiki ke amfani da shi wajen ci gaban rayuwa.
Comments
Post a Comment