AFENDIS
Ciwon Afendis: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani.
1. Afendis wato "appendix" a turance, wani ɗan zunɓutu ne mai kamar jela a mahaɗar ƙaramin hanji da babban hanji. Girmansa ya kai girman yatsan hannu.
2. A ina afendis yake? Afendis yana nan a ciki a kwiɓin dama daga ƙasan cibiya kaɗan.
3. A likitance, afendis ba shi da wani takamaiman aiki a jiki ɗan Adam. Sai dai, wasu masanan na cewa afendis na ɗauke da wasu ƙwayoyin garkuwar jiki waɗanda ke taimaka wa jiki yaƙi da ƙwayoyin cutuka.
4. Ciwon afendis, wato "appedicitis" a turance, ciwo ne da ke kama afendis yayin da afendis ya kumbura ko kuma ya ɓule bayan ruɓewa saboda wasu dalilai.
5. Abubuwan da kan haddasa kumburin afendis sun haɗa da: harbin ƙwayoyin cuta kamar bakteriya, toshewar bakin afendis daga dunƙulallen turɓayan abinci ko bayan gida, ciwon daji/sankara da dai sauransu.
6. Alamun ciwon afendis sun haɗa da:
- ciwo a kwiɓin dama, ƙasa da cibiya ƙaɗan.
- ciwo a kewayen cibiya wanda daga bisani kan zarce zuwa kwiɓin dama.
- ciwon da ke ta'azzara yayin tari ko wani yunƙuri.
- ciwo yayin da aka danna kwiɓin dama da cibiya.
- tashin zuciya da amai.
- Rashin sha'awar cin abinci.
- matsakaicin zazzaɓi, da sauransu.
7. Ciwon afendis na buƙatar tiyatar gaggawa domin cire shi, musamman idan ya riga ya ɓule ko kuma ana tsoron fashewarsa a kowane lokaci.
8. Barin ciwon afendis ba tare da an cire shi ta hanyar tiyata ba na da haɗarin gaske, domin ɓulewa ko fashewarsa na nufin fantsamar ƙwayoyin cuta da ke ƙunshe ciki zuwa dukkan sauran kayan ciki.
9. Hanyar kariya daga ciwon afendis: babu wata sahihiyar hanyar kariya daga ciwon afendis; sai dai masana kimiyyar abinci na ganin cewa ciwon afendis bai cika kama masu cin datsar hatsi, ganyayyaki da 'yayan itatuwa ba, wato masu ƙaurace wa sarrafaffen abinci kenan.
Saboda haka, batun cewa afendis gidan tsakuwa ne ko kuma ciwon afendis na faruwa ne yayin da tsakuwa ta cika shi tatsuniya ce kawai!
Comments
Post a Comment