AMFANIN GANYEN MANGWARO
*ABUBUWA GOMA DA GANYEN MANGWARO KEYI*
🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴🌴
1. Ganyen mangwaro na kawar da cutar siga wato ‘Dibetes’
Ganyan mangwaro na warkar da cutar siga ne idan aka shanya shi ya bushe sannan aka jika garin a ruwa sai a rika sha.
2. Yana kawar da hawan jini.
Ana yin amfani da garin busashen ganyen mangwaro, sai a rika diba ana dafa shi ana sha kamar shayi. Haka zai taimaka wajen kawar da hawan jini.
3. Yana warkar da cutar koda
Shan ruwan ganyen magwaro da aka jika na warkar da cutar Koda.
4. Yana warkar da matsalolin da ke han numfashi.
Idan aka hada ruwan ganyen mangwaro da zuma, ana samun lafiya ga mura da cutar Asma.
5. Yana kawar da atini.
Shima idan aka sha ruwan zai taimaka wajen dakatar da Atini.
6. Yana dakatar da shakuwa.
Mai fama da shakuwa zai warke idan ya shaki hayakin ganyen mangwaro.
7. Mai fama da rashin natsuwa wato ‘Anxiety’ zai samu sauki idan yana shan ruwan ganyan mangwaro.
8. Mai fama da ciwon ciki zai sami sauki idan yana shan ruwan dafaffen ganyen kullum safe kafin a ci abinci.
9. Yana warkar da ciwon kunne.
Ruwan dake cikin ganyen mangoro na dauke da sinadarin warkar da ciwon kunne wanda idan aka diga a kunnen dake ciwo zai warke.
10. Ganyen mangwaro na warkar da kuna
Ana amfani da tokan ganyen mangwaro a shafa a kan rauni don a warke.
*DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUPS*
📲08080678100
Comments
Post a Comment