AMFANIN KANUMFARI
*AMFANIN KANUMFARI GA MAZA DA MATA* ππππππππππ Amfanin kanunfari ga mata da maza kusan guda ne. Binciken da masana kimiyya da dama suka yi ya nuna cewa kanunfari na Ζara wa mata da maza ni'ima. Kanunfari na da amfani ga mata wajen inganta Ζwan haihuwa, sannan yana taimakawa wajen shawo kan matsalar rashin daukar ciki. Kanunfari na bunΖasa isar wasu saΖonni ga ΖwaΖwalwa waΙanda ke motsa sha'awa ga mata da kuma maza. Kanunfari na Ζara wa mata kuzari lokacin jima'i. Baya ga taimakawa wajen rage jiki yana sa rashin tsufa. Man kanunfari na taimaka wa mata wajen samun sauΖin ciwon mara a lokacin al'ada da taΖaita kwanakin al'adar. Amfanin kanunfari ga maza Kanunfari na Ιaya daga cikin magungunan gargajiya da ke Ζara wa maza lafiya domin kuwa yakan Ζara yawan sanadarin 'testosterone' wanda ke tasiri wajen haΙakar gaΙoΙin saduwa na namiji. Rashin isasshen sanadarin 'testosterone' a jikin namiji na iya haifar masa da matsalar rashin Ζarfin mazakuta,...