CUTAR DAMUWA

DEPRESSION
1. Depression ciwo ne da yake shafar zuciya da kwakwalwa. Mutane da yawa suna gani cewa depression shine mutum ya shiga matsala ko ya rika jin haushi da bacin rai na dan wani lokaci. Sai dai depression ya wuce haka. A turance depression yana nufin a danne wani a hanashi rawar gaban hantsi. Ko kuma Mutum ya shiga wani yanayi da bature yake cewa 'boredom', wato yanayi na rashin abun yi.

2. Sai dai abinda zamuyi magana akai shine Clinical depression, ana kuma kiransa da major depressive disorder ko, ko biochemical depression, ko endogenous depression ko biological depression ko kuma unipolar disorder. Duk wadannan sunaye ana amfani dasu wajen kiran irin depression da yake zama matsala ga rayuwar mutum sosai, ta yadda in ba asibiti akaje ba, dai dai abu yayi ta kara muni.

3. To yaya ake gane cewa mutum yana faama da clinical depression? "International Statistical Classification of Diseases and Related Health Problems 10th Revision (ICD-10)" wata hanya ce da WHO ta samar don gano alamomin ciwuka irin depression. A tsarin ICD-10, ana tabbatar da cewa mutum yana da clinical depression ne idan ya shafe akalla sati biyu dauke da alamomin clinical depression. Hakazalika sai wadannan alamomi sun zama ana tare dasu kullum ko kuma kusan kullum kafin a kai ga tabbatar da cewa akwai depression. Sannan ba za a tabbatar da clinical depression ba har sai wadannan alamomi (symptoms) sun zama suna kawo matsala ga tsarin rayuwar mai faama da clinical depression, kamar misali suna kawo matsala ga yadda yake gudanar da aikinsa, ko alakarsa da iyalinsa, ko sauran jama'a ko kuma sauran abubuwa masu muhimmanci ga rayuwar maras lafiya.A takaice dai dole wadannan matsaloli su zama sun mayar da tsarin rayuwar maras lafiya ya sha bamban da na sauran mutane.

4. Idan aka samu akalla biyar daga cikin wadannan alamomi a tare da maras lafiya  to za a tabbatar da cewa mutum yana faama da depression,

a. Baƙin ciki da debewar tsammani a rayuwa (hopelessness), da jin rayuwarka bata da ma'ana, wato mutum ya rasa abinda ke masa dadi a duniya. Idan hakan ya zamto yana faruwa a mafi yawan lokuta a rana, to za a lissafa shi a cikin alamomin clinical depression. Yara 'yan shekaru 13-19 (teenagers) kuwa, idan suna faama da clinical depression, sukan zama suna kasa zama guri daya, sannan suna tsananin saurin fushi da zafin rai maimakon bakin ciki da debewar tsammani irin na manya.

b. Mutum yaji kwata-kwata baya sha'awar al'amuran rayuwa da sauran mutane suke sha'awah. Haka kuma koda yayi wadannan abubuwa, ba zai samu farin ciki da jin dadi (pleasure) kamar yadda sauran mutane suke samu ba.

c.  Ramewa ga wadanda ba ramar suke nema ba (misali wadanda qiba tayi musu yawa suka rage cin abincinsu don su rageta-wato 'dieting' kenan). Ramewa da kashi biyar cikin dari na nauyin jiki (5% loss of body weight) ko sama da haka, yana nuni zuwa ga alamar clinical depression.

d.  Yin bacci fiye da kima ko kuma matsalar bacci da wahala wajen yin bacci ga wasu.

e. Yawan kai komo fiye da kima (psychomotor agitation), ko kuma rashin motsi da zama waje daya (psychomotor retardation) ga wasu.

f. Yawan gajiya ko kuma rashin karfi kusan koda yaushe ko kuma a mafi yawan lokuta.

g. Mutum ya rika ji kamar bashi da wata amfani a duniya (worthlessnes) ko kuma ya rika ji kamar yayi wani babban laifi (guilt).

h. Mutum ya kasa yin tunani ko kuma mayar ko hankali akan wani abu (lack of concentration), ko kuma ya kasa yanke wani hukunci (difficulty in decision-making) a rayuwa kamar yadda sauran mutane suke yi.

i. Yawan tunanin mutuwa; ya zama a ko da yaushe ko kuma a mafi yawan lokuta shi mutuwa yake tunani. Wasu daga cikin masu wannan matsala ba wai tsoron mutuwar suke ba, amma dai kullum cikin tunaninta suke, wasu kuma a cikin masu wannan matsalar suna tsoron mutuwa fiye da yadda sauran mutane suke, wato fiye da yadda hankali zai dauka.

5. Idan kuka dubi abubuwan da muka lissafo a sama, zaku gane cewa Depression babbar matsala ce mai sarkakiya. Idan ba kai kake faama da ita ba, ba zaka taba gane yaya mai faama da ita yake ji ba. Shiyasa wasu a cikin jahilci suke hantaran masu depression, a ganinsu ba rashin lafiya bane. Hakan ba karamin matsala yake jawowa ba. Yana sanyawa mutane su kare rayuwarsu cikin bakin ciki da damuwa, wasu ma har suyi tunanin kashe kansu. Ya zama dole a ilmantar da jama'a akan depression, don kowa ya gane cewa mai depression taimako yake nema ba hantara da cin mutunci ba. Zamuyi magana akan matsalolin da depression yakan haifar a rayuwar masu shi a yayin da aka gaza wajen daukar matakin da ya dace wajen maganceshi akan lokaci.

6. A kasashen gabashin duniya, an fi samun mata da depression fiye da maza ta yadda alkaluman bincike suka nuna cewa depression a cikin mata ya ninka wanda ke cikin mazaje har ninki biyu, sai dai maza sunfi kashe kansu akan depression, fiye da mata. Depression a cikin yara yana da wahalar ganowa. Yara masu depression sukan zama basa son cin abinci (loss of appetite). Sannan sukan zamo suna samun matsala a cikin rayuwarsu fiye da sauran yara. Misali sukan samu matsalar bacci ko su rika mugayen mafarkai. Ko kuma su rika samun matsala a wajen gudanar da rayuwarsu ko kuma a cikin sakamakon su na makaranta.

7. Depressions ya kasu zuwa kashi biyar:

a. Melancholia ko melancholic depression: depression ne mai muni. Yana jawo matsalar rashin cin abinci (loss of appetite) da matsalar bacci ko kuma mutum ya zama ya tsani ganin kansa cikin jama'a.

b. Psychotic depression yana kama da melancholia, sai dai shi yana sanya mai faama dashi ya zama yana rasa hankalinsa na wani lokaci. Ya rika ganin abinda mutane basa gani ko kuma abinda babu shi ma a duniya (hallucination da delusion).

c.  Atypical depression yana sanyawa mutum ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya zama yana birkice (anxiety) ko kuma cikin tsananin tsoro da razana (panic attack).

d. Chronic dysthymic disorder shima depression ne da bashi da tsanani amma akan shafe tsawon lokaci ana fama dashi. Yana farawa daga lokacin da aka balaga (adolescence), sannan akan shafe daga shekara biyar zuwa shekaru da yawa ana faama dashi.

e. Seasonal Affective Disorder (SAD) Depression ne da yake zuwa a lokacin sanyi (winter) kuma yake tafiya lokacin zafi.

8. Gano hakikanin abinda ke jawo depression ya gagara. Ana cigaba da tafka muhawara a tsakanin masana kimiyya akan abinda ke jawo depression. Sai dai dukkan muhawarar ta ta'allaka ne akan abubuwa guda uku:

a.  Wasu suna ganin cewa abinda ke jawo depression ya shafi al'amura ne na biology (biological factors). Wato samun canji na wasu sinadarai da suke kai-komo tsakanin kwakwalwa da sauran sassan jiki. Wadannan sinadarai ko 'yan aika su ake kira 'neurotransmitters'. Masu wannan bayani sunce samun canji ko matsala daga 'neurotransmitters' shike jawo depression.

b. Akwai wadanda suke gani yanayin tunani ke jawo depression. Suna ganin cewa idan mutum yana yawan yin tunani mai jawo bakin ciki (negative thoughts), to hakan zai haifar da matsala ga tsarin rayuwarsa, ya zamto yana jin haushin kansa da haushin sauran jama'a ba tare da dalili ba. Wadannan su suka kira da 'Cognitive factors'.  A cewarsu idan mutum yana tunani na rashin jin dadi da debewar tsammani (negative thoughts), hakan zai haifar masa da bakin ciki da kuma rashin jin dadin rayuwa da jin haushin mutane da sauran alamomin depression.

c. Akwai kuma wadanda suke ganin cewa matsalolin rayuwa irin su rabuwar aure, kora daga aiki, cutarwa ko cin zali (bully), talauci da sauransu su suke jawo depression. Wannan shi ake kira 'Socio-cultutal factors'.

9. Baya ga wadancan da aka ambata a sama, akwai abubuwan da ake zargin suna jawo depression:

a.  Gado: Ana ga cewa za a iya gadon depression a wajen iyaye ko kakanni ko kawunai da sauransu, sai dai sau tari akan samu masu depression wadanda a danginsu babu mai shi ko kwara daya.

b. Akwai chemicals (neurotransmitters) da suke aiki a kwakwalwa kuma suke lura da ayyuka daban-daban. Misali akwai chemical da ake kira 'serotonin' wadda shi ke kula da sashen farin ciki na kwakwalwa. Tsananin yawansa ko karancinsa yana haifar da depression.

c. Akwai al'amuran rayuwa da idan sun faru da mutum zasu iya haifar da depression; sun hada da mutuwar iyaye ko masu kula da mutum, guje wa mutum ko kuma a yasar dashi kamar almajirai da sauransu ko a ƙi mutum a cikin al'uma (abandonment, rejection, ko neglect), cuta ko rashin lafiya da mutum ya jima yana faama da ita (chronic illness), cutarwa da akayi wa mutum a jiki (ta hanyar duka da sauransu) ko ga zuciya (zagi da cin mutunci da hantara ko cin amana da sauransu), ko fyade ko kokarin tursasawa zuwa jima'i daga masu manyan matsayi ko alfarma (sexual abuse), da sauransu.
d. Matsaloli da suka shafi yanayin tunanin mutum, Kamar raina kai ko kuma raina abinda zaka iya, kana ji cewa baka kai ba, duk da a zahirin gaskiya ka wuce (low self-esteem).

e. Matsalolin rayuwa kamar su rashin aikin yi, rashin wajen zama ko wajen kwana kamar masu kwana akan hanya (homelessness), matsala da abokin zama ko abokiyar zama ko soyayya, ko rabuwa da abokiyar zama ko soyayya (kamar saurayi ya yaudari budurwa ko budurwa ta yaudari saurayi ko tsakanin mata da namiji ko cin amana da sauran relationship problems), cutarwa daga masu laifi kamar barayi da 'yan fashi da 'yan daba da masu fyade da sauransu da sauran matsaloli suna haifar da depression.

f. Akwai cutuka da suke haifar da depression kamar su hypothyroidism, hepatitis, mononucleosis, head injury da sauransu.

e. Shan giya da shan magunguna ba bisa ƙa'ida ba (drug abuse) kamar magungunan saka bacci da magungunan hana haihuwa  da sauransu suna iya haifar da depression.

g. Akwai magunguna da ake amfani dasu wajen kashe kwari (pesticides), binciken wasu masana ya tabbatar da yiwuwarsu na jawo depression.

Comments

Popular posts from this blog

*YADDA ZAKI MATSE GABANKI.. (FEMALE ONLY)* *Ana so ko da yaushe idan mijinki zai kusance ki yaji ki a matse kike, ba''a son lokacin da miji zai kusanci matarsa ya wuce siririf.* *Don haka ya ke da kyau mace ta rika kula da gabanta kar ya bude.* Abubuwan da ke matse mace suna da yawa misali ☛ Bagaruwan hausa. ....ana dafa ta da ganyen magarya ko ita kadai a rika wanke gaba dashi ko ki zuba a baho ki zauna a ciki da dumin kaman 30mins a kalla sau biyu a sati. . ☞ Kanunfari ana dafa shi a sha da zuma da zafi zafi ko ki jika ya kwana da safe ki tace kisha da madara da zuma. Ana kuma dafa ta a zauna a ciki da dumin ta ko a rika tsarki da ruwan ko kuma a zuba kanun farin garwashi a tsugunna shi ma sau 2 a sati Kwallon mangwaro idan kika fasa zaki ga dan ciki fari haka, ana busar dashi a daka a kwaba da zuma arika matsi da shi bayan isha'I idan zaki kwanta bacci ki wanke ko kuma ki dafa dan cikin da bagaruwa ki wuni tsarki dashi ko ki zauna a ciki n shima a kalla 3x a sati. ☞ Almiski fari ko ja ki daka kanunfari ki tankade yai laushi sai ki kwaba da miskin da man zaitun yawaita amfani dashi na matse mace sosai kuma kullum cikin kamshi....yana gyara macen da ta haihu sosai musamman da jinin haihuwa ya dauke ki fara amfani dashi har ki ar'bain... *Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da* ☞ ruwan dumi ☞ bagaruwa _Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki kuma wannan mun dade dayin bayaninsa._ ❀ *KAYAN HADIN* ❀ ☛ ki daka garin zogale ki tankadeshi. ☛ ki samu man ka danya ( Ana samu a wajen masu maganin gargajiya. ☛ ki samu man zogale ( Ana samu a wajen masu *_Islamic-medical-centre_*. ☛ ki samu Karo shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi ( Ana samun sa wajen masu kayan koli ). ☛ ki samu man shanu ( anansamunsa a wajen masu sa yarda nono). *duk ki hada su wajen daya ki kwaba su suyi kamar sa'oi 5awa zakiga sun hade sai Kiyi Matso dashi kuma Zaki iya rabashi uku gida 3 wato Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.* *HADADDEN MATSI MAI MATSE MACE YANDA KO YATSA BAZAI SHIGA BA INSHA ALLAHU* ☞ Ganyen magarya ☞ zogale ☞ bagaruwa ☞ ganyen bagaruwa ☞ alim ☞ sabulun salo ☞ sabulun zaitun ☞ sabulun habbatussauda. ☞ Miski ☞ madararturare. Zaki hade ganyayyakin da alim kidakesu saiki tankade ki dake sabulan saiki hadesu guri daya. Ki zuba miski da madarar turare ki cakudesu kisamu mazubimaikyau ki adana sai ki dinka gutsuro kadan kiwanko can zakiga yadda zai matse ko dan yatsa dakyar zai shigaba. *DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP* ☎08080678100

AMFANIN FUREN TUMFAFIYA

DOMIN SAMUN FARINJINI