TSARKI DA SABULU

ILLAR TSARKI DA SABULU
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
Da yawan mata na tunanin wanke al'aura da sabulu ko wasu sinadarai abu ne da yake da muhimmanci sosai, musamman don tsaftace wajen da a ko yaushe yake a rufe. Sai dai hakan ya yi muguwar illa ga wata mata a Najeriya.
Wannan dai al'ada ce da ta gama gari, alal misali, kiyasi ya nuna cewa kashi 20 zuwa 40 cikin 100 na matan Amurka da ke tsakanin shekara 15 zuwa 44 suna yawan wanke al'aurarsu da sabulu ko wasu sinadaran daban.
Duk da cewa a Najeriya babu wata kididdiga da ke nuna adadin matan da ke irin wannan abu, amma akwai tabbacin cewa al'ada ce da mafi yawan matan kasar ke yi don tsaftace kansu. Sai dai abin da yawancin mata ba su sani ba shi ne, hakan na da illa sosai ga lafiyarsu.
Hajiya Ladidi, wacce muka sauya wa suna, ta shaida min irin yadda yin tsarki da sabulu ya yi mata muguwar illa ga lafiyarta.
"Na kasance mace mai yawan son tsafta da kamshi, don haka ko yaushe cikin wanke tare da kalkale jikina nake musamman al'aura, wacce nake ganin rashin kula da ita na iya sa a dinga jin dan wari-wari na tashi".
Ta ce ta kan shafe kusan sa'a daya a bandaki idan ta shiga wanka, "don ina Ι“ata lokaci sosai wajen wanke al'aurata da sabulai kala-kala". Sannan tana fesa turaruka kala-kala.
"A duk yayin da na kammala al'ada kuwa to gyaran yana fin haka don har tsiyaya turaren miski nake a al'aurar tawa mai yawa ba dangwalawa a auduga ba, don ina son gyaran nawa ya fi na kowa."
Ka san illar yawan tsafta ?
Hikayata: Illar hana 'ya mace yin karatun zamani
Mijin Victoria ya so 'kashe ta saboda rashin haihuwa'
Sai dai ba a dade ana tafiya ba, sai ta fara ganin ba daidai ba, inda ta fara da "zubar wani ruwa kalar madara daga al'aurata", inda har ta "kafafuna yake zirara da yake ban faye sa Ι—an kamfai ba (Pant)".
"Wasa-wasa sai ga shi ya fara wari sosai ya kuma sauya kala zuwa kore-kore. Wani lokacin sai na dinga tsarguwa ko wanda ke zaune kusa da ni ma na iya jin warin.
Ladidi ta kara shiga cikin damuwa tana tunannin ko cuta ta dauko wajen amfani da ban-dakin da ba shi da tsafta a wani wajen.
"Don haka sai na fara tambayar mutane sai wasu su ce ko mijina ne ya kwaso cuta wajen matan banza ya shafa min, ni kuma can cikin raina gaskiya na yarda cewa mijina ba ya neman mata.
"A karshe dai na je asibiti a ka duba ni sai likitan ya bani gwajin ciwon suga don larurar tawa na daga cikin alamunsa, amma da sakamako ya fito sai a ka ga ba haka ba ne.
''Amfani da sirinji mara tsafta na janyo yaduwar cututtuka'
Ko Ζ™ayyade iyali na taimakawa bunΖ™asar tattalin arziki?
Nigeria: 'Likita ya datse' hannun wata jaririya a Kebbi
Daga nan sai aka tura ta wajen wata Ζ™wararriyar likitar mata a National Hospital da ke Abuja, inda ta ce tambaye ta ko akwai abin da nake yawan sawa a al'aurata.
A nan na ta shaida mata ba na ta komai amma tana son tsafta kuma ta kan wanke shi da duk wani sinadari da ake sayarwa don wajen ya yi kamshi.
A lokacin ne likita ta shaida mata cewa lallai wadannan abubuwa su suka yi min illa.
Ta sa ta tayi gwaje-gwaje da dama har da gwajin mahaifa na Pap Smear, inda aka gano kwayoyin cuta sun "kama Ζ™ashin Ζ™ugunta wanda aka fi sani da Pelvic Inflammatory Disease, hakan kuma na iya toshe mahaifa daga Ι—aukar ciki.
"A Ζ™arshe dai ta Ι—ora ni a kan magunguna da allurai na musamman har tsawon wata biyu, aka kuma sake wasu gwaje-gwajen a ka gano cewa cutar ta tafi. Amma fa na sha wahala gaskiya ba kaΙ—an ba."
Hajiya Ladidi ta ce min a yanzu haka ba ta wanke al'aurarta da komai da ya wuce ruwa, don kuwa ita ta ga abin da ta gani.
DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUPS
08080678100

Comments

Popular posts from this blog

*YADDA ZAKI MATSE GABANKI.. (FEMALE ONLY)* *Ana so ko da yaushe idan mijinki zai kusance ki yaji ki a matse kike, ba''a son lokacin da miji zai kusanci matarsa ya wuce siririf.* *Don haka ya ke da kyau mace ta rika kula da gabanta kar ya bude.* Abubuwan da ke matse mace suna da yawa misali ☛ Bagaruwan hausa. ....ana dafa ta da ganyen magarya ko ita kadai a rika wanke gaba dashi ko ki zuba a baho ki zauna a ciki da dumin kaman 30mins a kalla sau biyu a sati. . ☞ Kanunfari ana dafa shi a sha da zuma da zafi zafi ko ki jika ya kwana da safe ki tace kisha da madara da zuma. Ana kuma dafa ta a zauna a ciki da dumin ta ko a rika tsarki da ruwan ko kuma a zuba kanun farin garwashi a tsugunna shi ma sau 2 a sati Kwallon mangwaro idan kika fasa zaki ga dan ciki fari haka, ana busar dashi a daka a kwaba da zuma arika matsi da shi bayan isha'I idan zaki kwanta bacci ki wanke ko kuma ki dafa dan cikin da bagaruwa ki wuni tsarki dashi ko ki zauna a ciki n shima a kalla 3x a sati. ☞ Almiski fari ko ja ki daka kanunfari ki tankade yai laushi sai ki kwaba da miskin da man zaitun yawaita amfani dashi na matse mace sosai kuma kullum cikin kamshi....yana gyara macen da ta haihu sosai musamman da jinin haihuwa ya dauke ki fara amfani dashi har ki ar'bain... *Inda wannan ta faru dake Zaki iya tsarki da* ☞ ruwan dumi ☞ bagaruwa _Na tsawon Wata guda sai kuma matsi shi kuma zakiyishi saura sati biyu aurenki kuma wannan mun dade dayin bayaninsa._ ❀ *KAYAN HADIN* ❀ ☛ ki daka garin zogale ki tankadeshi. ☛ ki samu man ka danya ( Ana samu a wajen masu maganin gargajiya. ☛ ki samu man zogale ( Ana samu a wajen masu *_Islamic-medical-centre_*. ☛ ki samu Karo shine wanda ake tawada dashi kuma ana wanke hula dashi ( Ana samun sa wajen masu kayan koli ). ☛ ki samu man shanu ( anansamunsa a wajen masu sa yarda nono). *duk ki hada su wajen daya ki kwaba su suyi kamar sa'oi 5awa zakiga sun hade sai Kiyi Matso dashi kuma Zaki iya rabashi uku gida 3 wato Kiyi matsi dashi Sau uku a cikin sati biyu.* *HADADDEN MATSI MAI MATSE MACE YANDA KO YATSA BAZAI SHIGA BA INSHA ALLAHU* ☞ Ganyen magarya ☞ zogale ☞ bagaruwa ☞ ganyen bagaruwa ☞ alim ☞ sabulun salo ☞ sabulun zaitun ☞ sabulun habbatussauda. ☞ Miski ☞ madararturare. Zaki hade ganyayyakin da alim kidakesu saiki tankade ki dake sabulan saiki hadesu guri daya. Ki zuba miski da madarar turare ki cakudesu kisamu mazubimaikyau ki adana sai ki dinka gutsuro kadan kiwanko can zakiga yadda zai matse ko dan yatsa dakyar zai shigaba. *DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP* ☎08080678100

AMFANIN FUREN TUMFAFIYA

DOMIN SAMUN FARINJINI