DABARUN GYARAN JIKI
*HANYOYIN DA ZA'ABI DAN GYARA JIKI*
👳🏻👳🏻👳🏻👳🏻👳🏻👳🏻👳🏻👳🏻👳🏻👳🏻
♦Idan ana so a gyara gashi za a iya hada ayaba da dwai sai a kwaba su sosai sannan a shafa a gashi a jira na tsawon mintuna sha biyar zuwa talatin sannan a wanke.
♦domin gyaran farce, za a iya tsoma hannu a cikin man zaitun na tsawon mintuna biyar sannan sai a cire a kullum. Farce zai yi kyau sosai.
♦Ana amfani da zuma mai kyau domin samun fuska mai sulbi da laushi. Ana shafawa a fuska a jira na tsawon mintuna goma sha biyar zuwa ashirin sannan a wanke da ruwan dumi. A gwada wannan hadin sau daya a sati za a ga canji.
♦Ana amfani da ruwan amfuna da ruwa ana wanke kai. Yin hakan na cire dattin da ke madale a gefen gashin kai.
♦Domin masu yawan shafe-shafe za su iya yanka lemon tsami biyu sai su rida shafawa a inda ya yi duhu. Yin hakan a kullum na haskaka badin da ya bayyana a wasu gafen fata.
♦Domin samun fatar jiki mai sulbi, za a iya amfani da man zaitun da gishirin rafi a kwaba sai a rida dirzawa a fatar jiki a kalla sau uku a sati.
♦Man kwa-kwa na matudar gyaran zubewar gashin ka. Za a iya shafa man kwa-kwa a fatar ka, sannan a shafa a jikin gashin. A bari ya jima kamar na awa daya sannan a wanke.
♦Maza masu son man gyaran gemu, za su iya amfani da man kwa-kwa.
♦ A samu lemon tsami sannan a zuba zuma a kai.Sannan a rida shafawa a kan durajen fuska. Yin hakan na kasha su sosai.
♦Man zaitun na sanya santsin fata idan an kasance ana yawaita shafa shi a koda yaushe a matsayin man fata.
*MATSALOLIN MA'AURATA GROUP*
☎08080678100
Comments
Post a Comment