ABINDAKE BURGE MAZA
*MATARDAKE BURGE MAZA*
1♦Matar da ta yarda ita mace ce, don haka ta tanadi duk abin da ake bukata a wajan mace.
2♦Mace mai hikma da azanci, wacce ta karanci mijinta da kyau, kuma take kaucewa duk abin da zai haddasa matsala a tsakaninsu.
3♦Mace mai taushin hali da nutsuwa, wacce miji yake jin nutsuwa idan yana tare da ita.
4♦Mace da kudi bai dame ta ba, ita mijinta kawai take so, ko da akwai ko babu.
5♦Mace mai hakuri da juriya, babu gunaguni, babu mita, da kai kara ga iyaye ko kawaye.
6♦Macen da ta dauki kanta likita, mijinta mara lafiya, domin ya sami kulawa, ta musamman da riritawa.
7♦Mace mai saurin daukar ishara, tana gane shiru da magana, da motsi da yanayin shigowa da fita, samu da rashi da kuma yanayin da ake ciki a duniya ko a gari.
8♦ Mace mai sakakkiyar zuciya, mara kulli da ramuwa.
9♦ Mace mai karawa miji kuzari da karfin hali, a kan kyawawan manufofinsa.
10♦ Mace mai rikon amanar aure, da soyayya ga mijinta kawai.
*DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP*
☎08080678100
Comments
Post a Comment