MATSALOLIN ZAMA DA MACE DAYA
*ILLOLIN ZAMA DA MACE DAYA*
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
Zama da mace daya yana kawo illoli da dama ga magidanci da su mata kansu da kuma
al`umma.
****
*ILLOLI GA MAGIDANCI*
1:-Yana rage masa nishadin aure.
2:-Yana kawo tsufa da wuri.
3:-Yana saka maigida cikin damuwa
4:-Yana saka wa mace ta rika daga masa kai, tayi masa yadda taso saboda ta san ba shi da yadda zai yi.
5:-Yana rage masa samun soyayya da tarairaya da kulawa da ya cancanta a matsayinsa na maigida.
6:-Yakan hana shi tantance so na gaskiya daga bangaren matarsa ko wanin haka.
****
*ILLOLI GA SU MATAN*
1:-Yana hana wadansu samun mazajen aure.
2:-Yana dorawa matar gida aiyukan da suka shige misali kamar, kulawa da maigida, yaran gida da ita ma kanta.
3:-Yakan hana mace samun isasshen hutu da kuma lokacin kulawa da kanta.
4:-Yana rage wa mace kuzarin nuna soyayya ga maigidanta.
5:-Yana saka matar gida cikin tsoro da fargaba maras yankewa na ko za ai mata kishiya.
6:-Yana haifar da rashin amincewarta ga maigidanta da dauwamar da tuhuma ta har abada.
7:-Yana saka mace cikin shirin yaki da dawainiyar dakon makamai marasa ranar yankewa na nuna kin ayi mata kishiya.
8:-Yana saka mata yawan zargi ga dukkan matan da suke da alaka da maigidanta ko ma wace iri ce koda ma yar uwa ce ko abokiyar kasuwancinsa.
9:-Yana kara mata zafin kishi da rashin nutsuwa marasa ranar yankewa.
****
*ILLOLIN GA AL`UMMA*
1:-Yana haifar da karuwar mata marasa aure.
2:-Yana bunkasa yawan zawarawa acikin al`umma.
3:-Yana dorawa al`umma karin nauyin kulawa da mata iyayen marayu da marayun kansu.
4:-Yana bunkasa zinace-zinace a cikin al`umma.
5:-Yana rage tausayi da son bada taimako da agaji daga zukatan al`umma.
6:-Yana kara saka fargaba da tsoro a zukatan iyaye wadanda suke da `ya`ya mata a gaba.
7:-Yana bunkasa kasuwar malaman tsibbu da bokaye.
*DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP*
☎08080678100
Comments
Post a Comment