CUTUTTUKAN MA'AURATA
CUTUTTUKAN MA'AURATA
✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻✍🏻
1-DAUKEWAR SHA'AWA
Wannan wata cuta ce da Basir yake kawowa musamman ga ma'aurata, alamarta shi ne: Xaukewar sha'awa da ni'imar mace, qaiqayin gaba. Ko kuma raunin Azzakari wato rashin qarfinsa wajen gamsar da iyali, in yayi ma ba zai iya kawowa ba.
2-SANYIN MATA:
Alamar sanyin mata shi ne: Fitar farin ruwa ta gaba, rashin sha'awa, ciwon mara da qaiqayi da qurajen farji.
3-YANKAN GASHI:
Alamar yankan gashi shine rashin jin daxi yayin saduwa, jin zafi yayin saduwa da kuma tsagewar gaba.
4-BAQIN SANYI:
Alamar Baqin sanyi shi ne jin qaiqayi a jiki, jin motsin ciki, kamar kina da ciki. Ciwon mara in yayi nisa yana iya hana haihuwa.
5-ZAFIN MAHAIFA:
Idan zafin mahaifa ya yi yawa yana iya ruvar da Maniyyin da ya shiga cikin mahaifa wanda sanadiyar haka ciki ba zai samu ba.
6-SANYIN MAHAIFA:
Idan sanyi ya yiwa mahaifa yawa, in maniyyi ya shiga sai sanyin yai masa yawa sai yaqi bura saboda sanyin yayi masa yawa sai ya zarce kwana (40) bai canza daga maniyyi ba don haka sai ciki ya qi samuwa.
ALAMUN RASHIN HAIHUWA NA VANGAREN SANYI SU NE:
Fitar farin ruwa ta gaba.
Qaiqayin jiki da na farji.
Jin kamar wani abu na yawo a jiki.
Ciwon qirji, baya, zafin jiki da sauransu.
MAGANI:
A nemo saiwar zogale guda bakwai (7) Tafarnuwa guda tara (9) a haxa da garin hano a tafasa ta a dinga shan kofi xaya sau uku a rana. Sannan kuma a dinga yawan shan qwallon tafarnuwa da ma'ul-miyahi sau uku a kullum zata samu ciki a cikin wata uku Insha Allah.
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA
08080678100
Comments
Post a Comment