HADIN TATTABARA
TATTABARA UWAR ALQAWARI 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 Masana sun tabbatar cewa hadin da ake amfani da shi da naman Tantabara, babu shakka yana dadewa a jika. Ga yadda ake hadin:
1. Za ki samu Tanbaru guda biyu (Mace da Namiji)
2. Habbatus-Sauda (Cokali biyu)
3. Garin Raihan (Cokali hudu)
4. Ridi (Cokali uku)
5. ‘Ya’yan Zogale (daidai misali).
Bayan kin hada wadannan kayayyakin, sai ki dora a wuta, amma kada ki saka gyararrun Tantabarun tukunna. Har sai bayan sun dahu, ki sauke, ki tace ruwan, sannan ki kara dorawa, ki kuma hada da Tantabarun a cikin tukunyar, ki saka duk kayan kamshin da kike amfani da su. Bayan ya dahu daidai misali, sai ki sauke, ki cinye duka ke kadai DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
QASAITACCIYAR MACE 🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺🌺 shawarwari guda goma da ya kamata mace me fama da kuragen fuska tayi amfani da koda daya ko biyu daga ciki
(1) Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. kuma Ba kowane irin man goge baki
za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man
goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har
zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki.
(2) Ki kasance mai yawan shan
ruwa.yawaita shan ruwa ba wai zai sanya miki
laushin fata ba ne kawai, a’a, zai
taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka
yana da kyau ki guji yawan cin
abincin gwangwani, kasancewar
suna dauke da wasu sinadarai da za su rika sanya kurajen fuska. Ya
kamata ki yawaita cin ‘ya’yan
itatuwa da suka hada da su abarba da lemu da ayaba da kankana da sauransu.
(3) Ki rika amfani da grem irinsu ‘
(Jane Iradale) da (Neutrogenia Rapid Clear) da (Acne Eliminating Spot Gel)
da sauransu, hakan zai taimaka miki wajen daidaita man da ke fatarki, wanda masana fata suka ce idan yayi yawa yakan haifar da kurajen fuska.
(4) Ki kasance mai amfani da man
(Cornmeal) a fuskarki, yakan sanya kurajen fuska su motse sannan a hankali su bace, misali man shi ne (Intagilo Clear Sal Cleanser.) Sannan ki rika amfani da man da ke hana
yaduwar kwayar cutar bakteriya, irin wannan man yakan ratsa kofofin da suke fatar fuskarki da ma jikinki gaba daya, sannan yana yakar kwayoyin cutar da suke fatarki, a lokaci guda ya daidaita miki yawan man da yake fitowa daga fatarki. Zai kuma cire
miki kwayoyin halittar da suka mutu a cikin fatarki. Misalinsu; (Phytomer Gommage) da Luffa-0.
(5) Yana da kyau ki ware wata rana ko wadansu ranaku a cikin mako ba tare da kin shafa kayan kwalliya a fuskarki ba, hakan zai bai wa fatar fuskarki samun‘yancin shigar da kuma fitar da iska ta kofofinta ba tare
da wani cikas ba. Haka idan za ki
shafa kayan kwalliyar a fuskarki, to kiyi amfani da kayan kwalliyar da basa toshe kofofin fatar fuska.
(6) Ki kasance mai shafa mai domin fatar fuskarki ta kasance cikin danshi kasancewar wadansu kurajen fuskar sun fi bata fuska idan fuska tana bushe.
(7) Yi amfani da man (Tea Tree’)
domin ba wai kawai yana baje
kurajen fuska ba ne, a’a yana rage
karfinsu da kuma kalarsu. Za kisami ire iren wadannan man a shagunan sayar da kayan kwalliya na zamani
(8) Ki kasance mai yin taka tsan
tsan wajen amfani da ire iren man
shafawar da kike amfani da su a
gashin kanki, ma’ana kada ki sake ya rika taba fuskarki hakan zai iya haifar miki da kurajen fuska, kasancewar wadansu sinadaran an yi su don su
taimaka wa gashin kai ne, don haka idan suka shiga kofofin fatar fuskarki sai su haifar miki da matsala.
(9) Ki kasance mai gasa kurajen
fuskarki Duk lokacin da kurajen
pimples suka fito miki sai ki samu
wani kyalle mai tsafta, sai ki tsoma shi a ruwan zafi, ba wanda ya tafasa ba, bayan kin tsoma sai ki fito da shi sai ki rika dora shi a kan wajen da kurajen suke, sannan ki rika gogawa a hankali, zafin kyallen yakan sa kurajen su motse daga nan su mutu.
(10) Ki guje yin amfani da hannunki
wajen fasa kurajen da suke fuskarki, domin hakan yana kara yawansu
hade da sanya fuskarki ta kara
cabewa. DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
YADDA ZA'A MAGANCE KURAJEN FUSKA 👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼👩🏼
Matsalar kuraje da tabon fuska sun fi shafar matasa, mata da maza. Wani lokaci sai an sha wahalar magance kurajen fuska, amma sai tabo ya ki bacewa. Rashin bacewar tabo a fuska na bata kwalliya. Sau da yawa za a ga ba a son shiga taron mutane domin wadannan tabon.
Da yawan mutane sun gwada mayukan kantin, domin rabuwa da tabon fuska. Wasu sun yi sa’a wasu kuma ba su yi sa’a ba.
A yau mun zo da bayanin yadda za a magance tabon fuska. Muna son a san cewa daya za a zaba daga cikin hanyoyin da muka lissafo, kada a hada su gaba daya. Domin yin hakan zai kara lahanta fuska ne.
· A samu ganyen dogonyaro, sai a hada shi da kurkum, sannan sai a shafa a fuska. A jira tsawon minti 15, sannan a wanke da ruwan dumi.
· Za a iya shafa markadadden dankalin Turawa a kan tabo. Hakan na magance kurajen fuska, sannan ya hana su sake fitowa.
· A daka tafarnuwa sai a shafa a kan tabo. Tafarnuwa tana wari, amma tana gyara fuska, sannan ta magance tabon fuska.
· a hada karas da tafarnuwa da zuma sai a shafa a fuska na tsawon minti 20 kafin a wanke.
· A samu hodar ‘baking soda’, sai a hada ta da ruwa, sannan a shafa a fuska zuwa minti 2 ko 3, daga nan a wanke fuska da ruwan dumi DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
Comments
Post a Comment