AMFANIN ALBASA GUDA 10
1. Maganin Tari, Mura Ko Ciwon Makogoro.
Daga cikin amfanin albasa ga dan-adam akwai maganin sanyi, mura ko ciwon makogoro. Duk wanda ke fama da daya ko duk ciwon da muka zana a sama, musamman wanda ke fama da tari ko mura mai tsanani, ya nemi man Albasa cikin babban cokali 9, da zuma babban cokali 9, sai ya zuba man albasar cikin zumar ya gauraya sosai, daga nan sai ya samu mazubinsa mai tsafta kuma mai murfi ya adana ya arika shan cokali uku a kullum, wato safe, rana da dare.
2. Maganin Zafin Fitsari.
Ana amfani da albasa don magance matsalar fitar fitsari da zafi. Ga mutumin da ke shan wahala wajen fitar fitsari, ya nemi man albasa ya hada da zuma mai kyau da lemon tsami ya gauraya, ya tabbatar sun gaurayu sosai, sai ya dinga sha sau biyu a rana, ma'ana da safe da yamma, sannan kuma ya rika shafa man albasa ajikin mararsa.
3. Maganin Sanyin Kashi
Albasa na maganin sanyin kashi. Duk mai fama da wannan matsala ta sanyin kashi , sai ya samu albasa ya dafa Albasa ya dafa ta, ya zuba man zaitun a rika dumama wajen da ya ke jin ciwon, sannan da dare kafin ya kwanta barci sai ya shafe wajen ciwon da wannan hadin, sannan kuma ya rinka sha da safe, haka za ayi har tsawon kwana bakwai. In sha Allahu za'a dace.
4. Maganin Maruru Ko Kuraje.
Hakanan, daga amfanin albasa ga lafiyarmu, har da maganin kuraje ko maruru. Yadda za a yi shine, a samu albasa a kirba ta, sai a hada da man zaitun a dafa ake wanke marurun ko kurajen, bayan an kammala wanke wa, sai a shafa man zaitun a gurin.
5. Maganin Zubar Gashi.
Ina matan da ke fama da zubar gashi? Sai mu ce kayanku ya tsinke a gindin kaba, saboda za ku iya yin amfani da albasa domin magance wannan matsala. Duk matar da ke fama da zubewar gashi, ta samu ruwan albasa, ta hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ta dinga shafewa kanta da shi, ta tabbatar ta game kanta tun daga matsirar gashinta. Za ta yi haka a kullum kafin ta kwanta barci. Idan gari ya waye sai ta wanke da ruwan dumi. Haka za ta yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji za ta samu biyan bukata.
6. Maganin Lagwada.
Amfanin albasa ga lafiyar dan-adam ya hada da tasirinta wajen maganin kurajen lagwada, idan mutum na fama da wannan matsala, sai ya samu ruwan albasa ya hada shi da ruwan Kahl a saka a wajen a daure sai bayan kwana daya ko biyu sai a kwance idan bata cire ba sai a maimaita har sai ta cire. Allah Ya sa mu dace,amin.
7. Maganin Karfin Mazakuta.
Masana sun nuna cewa, daga cikin amfanin albasa ga lafiyarmu, akwai maganin karfin maza. Ga mai son ya amfana da wannan fa'ida ta albasa sai ya samu kofi daya na ruwan zuma mai kyau, marar hadi da rabin kofi na ruwan albasa, sai ya zuba cikin tukunya ya dora kan wuta idan ya fara tururi sai ya sauke sai a rinka shan babban cokali daya sau 3 a kullum.
8. Maganin Amosanin Ka.
Har-ila-yau daga cikin amfanin albasa ga lafiyar dan adam, har da maganin amosanin ka, duk matumin da ke fama da amosanin ka, sai ya samu ruwan albasa, ya hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ya dinga shafewa kansa da shi, ya tabbatar ya game kansa tun daga matsirar gashi. Zai yi haka a kullum kafin ya kwanta barci. Idan gari ya waye sai ya wanke da ruwan dumi. Haka zai yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji zai samu biyan bukata.
9. Maganin Daji (Cancer) Na Fata.
Ana yin amfani da albasa wajen maganin ciwon dajin fata. Idan mutum ya na fama da wannan matsala sai ya samu ruwan albasa, da garin hulba da karamin cokali na farar wuta. Zai hada ruwan albasar da garin hulba da kuma farar wutar waje guda ya gauraya su, sai ya ke shafawa a wajen ciwon safe da yamma tsawon mako biyu.
10. Albasa Na Taimaka Wa Ma Su Ciwon Sikila.
Daga cikin irin amfanin albasa ga lafiyar bil adama, akwai taimaka wa ma su fama da cutar sikila. Idan mutum na fama da wannan matsala ta sikila sai ya rika yanka albasa tare da ganyen Zogale yana ci. Insha Allahu, zai samu saukin ciwon Sikila din.
11. Albasa Na Inganta Lafiyar Jikin Dan Adam.
Bayanin masana ya tabbata kan yadda albasa ke inganta lafiyar jikin bil adam. Duk mutumin da ke fama da matsalar karancin jini, ya yawaita cin albasa. insha Allahu jininsa zai yawaita.
12. Albasa Na Taimaka Wa Mai Ciwon Siga.
Mai fama da ciwon siga zai iya amfani da albasa don samun sauki musamman a yanayin fitar fitsari da yawa cikin dare. Saboda haka duk mai fama da yawan fitar fitsari sakamakon ciwon Siga ya nemi albasa mai kyau ya rika yankawa kullum yana ci. Idan Allah Ya so, sigansa zai sauka, kuma zai dena yawan fita fitsarin.
13. Albasa Na Maganin Kwarkwata.
Amfanin albasa ga lafiyar dan adam, ya hada da maganin kwarkwata, duk matar da ke fama da kwarkwata, sai ta samu ruwan albasa, ta hada da man Simsim, da kuma garin Baqadunas, ta dinga shafewa kanta da shi, ta tabbatar ta game kanta tun daga matsirar gashi. Za ta yi haka a kullum kafin ta kwanta barci. Idan gari ya waye sai ta wanke da ruwan dumi. Haka za ta yi har tsawon mako guda. Da yardar Ubangiji za ta samu biyan bukata.
*DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUPS
08080678100
Comments
Post a Comment