HALAYEN MAZA
📝DABI'AR MAZA📝
💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟💟
Daga cikin mafi girman korafin da mata suke yi game da maza, shi ne, MAZA BA SA SAURARAR MAGANARSU: wato ba sa barin su su yi magana son ransu a kan matsalolunsu ko na gida. Daga sun fara sai su katse su.
Yayin.da su kuma maza suke yawan korafin cewa, MATA SUNA SON CANZA MUSU RA'AYI TA KARFI.Wato idan yana yin wani abu ko ya dauki wata matsaya ko ya yi wani yunkuri, sai ta zo ta shigo ta yi kane-kane a ciki. Ta rika nuna kamar ita ta fi shi sanin yqdda ya kamata ya tsara al'amuransa. Wani lokacin har ka ji wasu kan ce, "Sai ka ce ita ta haife ni."
Amma lallai da a ce maza da mata sun fahimci yadda suka sha bamban a dabi'u da yadda suke kallon lamuran rayuwa, hakika da wadannan korafai ba su yawaita haka ba.
DABI'AR MAZA
Namiji, mutum ne wanda a halayyarsa yake da son a ganin ya zama garkuwa a gidansu ko a gidansa, yana da son ganin ya iya komai da ake yi a gari, musamman na jarumta. Ya 'ki jinin a ce ya gaza a kowane fanni. Yana son a danganta shi da kwarewa. Yana kuma kwarewarsa ta bayyana, shi ya sa za ka taras yawancin ayyukansa suna da inifo (uniform) wanda daga gani za ka fahimci kwarewarsa. Misali injiniya ko likita ko soja da 'dan sanda da sauransu.
Duk wani abu da ya shafi ragwantaka ba ya son siffantuwa da shi. Domin yana da matukar son a girmama shi.
Maza ba su cika damuwa da karance-karancen littattafan da suka shafi soyayya da zamantakewa ba, kamar yadda mata kan yi..Bar su dai sun fi dagewa a fannonin wasanni da kere-kere da gine-gine da abubuwan suka shafi kasuwanci da sabbin kirkire-kirkire da sauransu.
Kasancewarsa mai son a ce ya zama rumfa-sha-shirgi a gidansa. Burinsa shi ne duk wani nauyi ko matsala ta gidan, shi ne zai samar da hanyar warware ta. Don haka daga lokacin da ya ji 'kyas, zai fara tunanin ya za a yi a sami mafita cikin gaggawa. Shi sam bai yarda da jinkirta warware matsala ba, kuma a wurinsa daukar matsalar gidansa a yi ta janjaninta ko a dauke ta a fitar da ita daga gidan don neman mafita ma gazawa ce.
INDA RIGIMAR TAKE⇨
Ita mace idan tana da matsala tana kawo maganar sau da dama don ta tattauna ta da wani makusanci ko masoyinta wanda ta damu da shi. Ko da kuwa ta san ba lallai ne a sami salution ba. Amma tattaunawar a nuna an damu da halin da take ciki yana rage mata damuwa kwarai.
Amma shi Gogan daga zarar ya ji matarsa ta kawo korafi, nan da nan sai ya shiga ba ta shawarar hanyar warware matsalar. Domin shi a tasa dabi'ar yana ganin babban aikin da ya kamata kenan. An sami matsala kuma ya kawo hanyar warware ta. Yayin da ita kuwa matar abin da za tai tsammani kawai shi ne, yana katse ta in tana magana ne saboda ba ya son sauraren ta.
DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP
☎08080678100
Comments
Post a Comment