YADDA ZAKIYI AMFANIDA HERBAL OIL
AMFANIN OILS ATAKAICE
🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯🍯
☆ZATULLAUZ
yana magance matsalolin fata kamar hanata bushewa kokuma oily face yana gyara gashi yahanashi karyewa.
☆ZAIT JAUZULHIND
yanagyara gashi kuma yana magance matsalolin basir
☆ZAITUL JIRJIR
idan akahadashi khal yana ni'imta gashi yayikyau kuma yahanashi zuba
☆ZAITUL HENNA
Yanasa bakin gashi yahana fitowar furfura yana maganin matsanancin tari.
☆ZAITULWARD
yana magance tari yana hana kaikayinjiki yanagyara fata
☆ZAITULHARMAL
Yana magance ciwon gabobi yana magance cututtukandake hana bacci yanamaganin sanyi.
☆ZAITULGAR
domin ciwon gabobi da matsalolin fata.
☆ZAITUL BANAFSAJ
yana fitodaga gashi aduk inda akashafashi yana kawo nishadi da walwala ajiki.
☆ZAIT IKLILUL JABAL
don magance amosanin kai
Daga cibiyar bincike ta
BIRNIN MAGAJI ISLAMIC CENTER
Rijiyar zake kano 08080678100
CIWON MARA KO CIWON CIKI
📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖📖
idan mace tana ciwon mara ko ciwon ciki
a lokacin al’ada ko jinin yari kayi mata wasa
⇨ zuma cokali 5
⇨ man tafarnuwa cokali 2
in an hada sai ta rika sha cokali 1 DA safe 1 da yamma.
MATAR DA JINI YAKI DAUKE MATA
ta rika shan man tafarnuwa rabin karamin cokali Sau 4 a rana.
MATAR DA TAKE DA KURAJE
a gabanta ko take jin kaikayi
a samu man tafarnuwa cikin karamin cokali sai ta matsa lemon tsami daya a cikin sannan ta rinka dan gwala da auguga tana shafawa a gabanta kwana 5 zata warke Insha ALLAH
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
[11/5, 7:19 AM] admin: ABUBUWAN DA ZAKI KULA DASU YAYIN DA KUKE SHIRIN AURE DA SAURAYINKI
🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻🙍🏻
Bayan kin fahimci Saurayinki kunyi soyayya da Hira irin wacce Musulunci ya umurce ku kuyi, abu na gaba shine Ku fara Maganar Aure domin kuwa Babu amfanin soyayya Da Saurayi idan har ba Aure zakuyi ba. Kuma musulunci bai yarda da irin wannan Soyayya ba ko in ce Tarayya, tsakanin Da Namiji da Mace.
Abun da ya kamace ki kiyi a Yayin da suke soyayya da Saurayinki shine, Idan har aka kai matsayin da Soyayyar ku tayi nisa ki fara masa maganar Aure domin A fara shirye shiryen Auren Naku. Hakan zaisa idan ma ba da gaske yake ba ko kuma bai shirya ba zaki gan ya fara ja baya akan soyayyar ku. Idan kuma ya shirya sai ki tabbatar kun Tsara komai kamar yadda Addini ya tanadar.
Idan kuma ya amince aka fara maganar Auren naku, toh abinda ya kamace ki kiyi shine, kada ki kuskura ki saka Karya a cikin Hidimar bukin ku domin kuwa wannan shine babban kuskure da Ma’aurata sukeyi kamin Aure. Ki tabbatar da bakiyi kokarin yin abunda yafi karfi matsayin Gidanku ba, domin wannan na iya saka ki cikin damuwa a gidan Auren ki.
A duk lokacin da za’ayi aure yana da Mahimmanci musan cewa Addini ya riga ya tsara mana komai cikin Sauki, Sannan kuma akwai Al’adu daban daban wanda kuma idan har basu sabawa addini babu matsala za’a iyayi. Dan haka idan akwai wata al’ada da kike sha’awar yi amma babu halin yi a Gidanku, kuma Mijin baida halinyi KADA KI KUSKURA ki matsa masa akan sai anyi wannan al’adar domin kuwa Albarkacin Aure yafi yawa ga Auren da aka gina shi akan Tausayin Juna. Kuma Saurayin naki zai fi ganin Mutuncin ki da na gidan ku a yayin da yasan cewa Baki matsa mishi akan abunda yafi karfin sa. Wannan Wani babban kuskure ne da Wasu Mata keyi tun kamin su shiga gidan Auren su, ganin anyi wani abu a bikin wance itama tanaso ayi a nata bukin.
Kada ki manta Tausayin Juna wani abu ne mai Mahimmanci a Zamantakewa, Sannan Gaskiya da Rikon Amana, ki tabbatar da Bakiyi wani abu ba domin burgewa ba sai dai dan Allah da kuma Irin soyayyar da ke tsakanin ki da shi Saurayin naki.
Allah sa mu gane gaskiya.
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
SALON JANHANKALIN MIJI📚📚📚📚📚📚📚📚📚
Masana sanin soyayya da jimai sun yi ittifaqi
akan
cewa macen data iya kissa itace mace.
Macen
dabata iya kissa ba to da sauranta kuma ko a
wajen
kwanciya tana zama koma baya. Idan kinason
kijanye hankalin mijinki gaba daya ko yaushe
yayita
tunaninki to ga hanyar dazakibi ko yaushe
kizama
kina cikin ransa kamar kaya a maqogoro
Zaki sami turare na madara mai kamshi
yazama
turarenki na kwanciya ne kawai bakya
kwanciya
batare da kinshafashi shiba.Saiki bari me
house
yasaba da kamshin sosai sannan saiki sami
under
wear dinsa batare da yasaniba ki shafesu da
wannan turaren naki.To wlh duk sanda yaje
yin
fitsari yaji wannan kamshin saikin fado a
ransa.
Take zaituno last moment dinku na dare. So
daya
tina zaiji bashida wani abu agabansa sai yazo
kikuma jiyar dashi wannan dadin. Wlh ko
kishiyace
dake soyake kawai girkinki yazagayo. DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 0808067810INGANTACCEN HADIN AMARE 💁🏼💁🏼💁🏼💁🏼💁🏼💁🏼💁🏼💁🏼💁🏼Ina amare dasuke daf dashiga gdajensu? ina uwar gda dakeson bawa me gda mamaki? ina wacce ni'imarta tadauke?uhm to munyomuku odar ingantaccen sinadarinda y'an sudan kecewa تهنئة Tahni'a sinadarine me dadi a baki mesaurin aiki ajiki yakawo ni'ima yadawoda sha'awa maza kuma yakaramusu kuzari da ruwan maniyyi mata da maza kowa zai'iya shan way'annan sinadarai da basuda illa anhadasu da ingantattun kayan islama uhm uwar gda ko amaryar da takusa aure kujarraba kusha mamaki
****************************
Ina y'an mata da amare da uwar gda to ga ingantaccen sinadari don gyaran brest maganine dabashida illa saima dada kyawun fata yaciko brest dinki wannan sinadari munsamasa suna TAUSI'USSADAR haka kuma munada ingantacccen maganin ni'ima cikin sauki yana kara ni'ima sosai yasanya jindadi danishadi tsakanin ma'aurata uwargda da amarya kunemeshi zaihanamuku jin zafi wajan mu'amala kuma yana kashe matsalolin gaba sunan wannan sinadari NI'IMATUZZAUJAINI
Munada ingantattun magungunan sanyi dasauran matsalolin mata
Muntanadi duk wasu sinadarai da kayan gyara marasa illa ga rayuwarku akwai kaya iri iri musamman matsalolin ku dasuka shafi matsalar al'ada da ciwonmara akwai kuma ingantattun tiraruka na humra domin kamshin jiki
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA 08080678100
A AYOYIN DA AKAFI SO AKARANTA KO A RUKIYA NE KO WARWARE SIHIRI
📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝📝
* Ta'awizi da Basmala
* Fatiha
* Aya 5 Tafarkon Suratul Bakara
* Ayoyi 2n Tsakiyan suratul Bakara, Wa ilahukum ilahum wahid lailaha illa huwa Ayatulkursiyyu Suratul Bakara 255
* Aya 3 na karshen Suratul Bakara wato a manarasul 285-286
* Shahidallahu a cikin Alimran aya ta 18-19
* Inna rabbakumullahi Ladhi khalaqas samawati wal ardh. . . A cikin suratul A'araf aya 54-56
* Afa hasibtum Annama Khalaqanakum Abasan cikin suratul Mu'minin 115-118
* Wa annahu ta'ala jaddu rabbina mattakhadha. . ." a cikin suratul jinni aya ta 3-9
* Ayoyi 10 na farkon Suratul Saffat
* Aya 3 na karshen Suratul Hashiri Wato "Lau anzalna hadhal Qur'ana. . . ." aya ta 21-23
* Qulhuwallahu ahad sau 3
* Fallaqi sau 3
* Nas sau 3 Domin wadannan ayoyi Annabi yayi amfani da su. Ubayyu ibn ka'ab ya ce bayan Annabi s a w ya karanta wadannan ayoyi sai mukaga maral lfy ya mike ya tashi kamar bai taba yin rashin lfy ba. Wato dai wannan Aljanin yafita daga jikin sa wannan dalili ya sa muke amfani da wadannan ayoyin amma dukkan ayoyin Al'Qurani waraka ne, amma wadannan ayoyi suna azaptar da Aljani sosai.
DAGA DANDALIN AMINU YAHUZA
08080678100
MATSALOLIN ALJANU DA YADDA ZA MAGANCE SU.
👹👹👺👺👹👹👺👺
Dukkan godiya da yabo su tabbta ga Allah madaukakin
sarki, tsira da aminci su tabbata ga Annabi Muhammad da
alayensa da sahabbansa da wadanda suka biyo bayan su
da kyautatawa har ya zuwa ranar tashin alkiyama.
Bayan haka wannan sako ne na musamman zuwa ga 'yan
uwa musulmai maza da mata dangane da matsalolin da
suka shafi matan aure da 'yan mata musulmai da samari
marasa aure da magidanta baki daya, dangane da
matsalar shafar Aljanu, da yadda suke shiga jikin mutum
dan Adam, da alamomin da dan Adam zai gane cewa
akwai Aljanin a jikinsa, sa'annan bayani game da matsalar
da ake kira (jinnul ashik) namijin dare ko (jinnu ashika)
macen dare.
Allah na ke roko ya mun dace wajen wannan rubutun
amen.
SU WAYE ALJANU KUMA DAGA INA ALLAH YA HALICCE
SU?.
Aljanu hailttu ne da Allah (SWA) ya yahalicce ya ajiye su a
duniya don su bauta masa.
Sa'annan ya halicce su ne daga harshen wuta, Allah (SWA)
yana cewa :
"KUMA YA HALICCI ALJANI DAGA WUTA (Harsashen
Wuta)".
Dan Abbas y ace lallai Aljanu an halicci su daga harshen
wuta.
Don haka sai muce Aljanu wasu halittu ne da Allah ya
halicce su daga harshen wuta, shi yasa ba a iya ganin su,
kuma ba a iya taba su ko jin mosinsu, saboda su ruhuine
kawai, bas u da tabbataccen gangan jiki irin na dan Adam,
shi yasa suke shiga surar irin jikin da suka ga dama,
kamar Kare, Maciji, Kyanwa (Mage), da sauransu.
NAU'IN HALITTUN ALJANU.
Allah (SWA) ya halicci Aljanu da nau'in halitti
mabanbanta.
An samo Hadisi daga Aba Sa'alabatal Kushaniy (RA) yace,
Manzon Allah (SAW) yace: "ALJANU NAU'I UKU NE (Wasu)
NAU'IN MASU FIKA FIKAINE, SUNA TASHI SAMA, DA
NAU'IN MASU ZAMA MACIZAI DA KUNAMAI DA MASU
ZAMA WURI DAYA SU KAURA" (Hakim ya fidda shi).
WURAREN DA ALJANU SUKE ZAMA
Sun kasance suna zama a cikin wadannan wuraren kamar
haka:-
1. Cikin Daji.
2. Cikin Ruwa.
3. Tsaunuka, da Koguna.
4. . Bayan Daki
5. Bola (Jibji).
6. Wajen Wanke – Wanke.
7. Wurin Makabarta.
Masu zama a cikin jama'a sun fi cutar da jama'a, saboda
suna zama a wuraren kazanta, shi yasa mafi yawan
cutarwar da Aljannu ke yi wa dan Adam su ne ke yi!! (Allah
ya tsare mu).
DALILIN DA YASA ALJANU KE SHAFAR DAN ADAM.
Yawancin Aljanu suna shafar dan Adam ne ta daya daga
cikin wadannan dalilai guda 4:-
1. Saboda zalunci da muguntar Aljanin.
2. Da sunan kauna ko son da Aljani ke yi wad an Adam,
kamar Aljani ya so mace mutum, ko Aljana ta so namiji
mutum.
A gaba za mu yi bayani akan wannan matsalar, kuma shi
ake kira da Jinnul Ashik (Namijin Dare) ko Jinnul Ashika
(Macen Dare) insha Allahu.
3. Saboda cutarwar dad an Adam ya yi wa Aljanun, kamar
ya zuba masa rowan zafi ko ya taka shi, sai ya zo daukar
fansa.
4. Ko Bokaye da matsafa su turo wa mutum Aljanin.
CUTARWAR DA ALJANI KE YI WA DAN ADAM.
Aljanu na cutar dad an Adam ta hanyoyi guda 2, kamar
haka:-
1. Ta hanyar shiga jikin dan Adam:- Shine Aljani ya shiga
jikin dan Adam gaba daya ko wata gaba, kamar hannu,
kafa, Baya, Kirji, Kai, Ido ko Kunne, sai yayi ta cutar da
marar lafiya yana wahalar das hi.
Wannan ya tabbata a cikin Hadisi, Manzon Allah (SAW)
yace:
"LALLAI SHAIDAN (ALJANI) YANA GUDANA A JIKIN DAN
ADAM AKAMAR YADDA JINI YAKE GUDANA".
Ma'ana: Yana iya shiga duk inda jinni zai shiga, saboda
bas hi da gangan jiki da zai hana shi hakan.
2. Ta hanyar Shafar jikin dan Adam:- Shine ya sanya ciwo
ko kuma ya lalata wata gaba daga cikin gabobin dan
Adam, kamar ya lalata ko shanye hanu, ya sanya ciwo ko
ya kurumtar da kunne, ko ya rike muryar mutum ko ya
sanya wa mace ciwo a mara ko mahaifa, ko ya taba mata
wata jijiya sai jinni ya yi ta zuba, da sauransu.
Irin wandannan Aljanun ba a samunsa a jikin marar lafiya,
sai dai ayi ta amfani da magani wadda musulunci yayi
umurnin amfani das hi, ta kuma hanyar mai kyau.
LOKOTAN DA ALJANI KE SHIGA JIKIN DAN ADAM.
1. Yayin da mutum yake cikin matsanancin bacin raid a
fushi.
2. Yayin da mutum ya tsorita.
3. Yayin da Mutum ya nitse cikin sabon Allah, kamar
kallace-kallacen fina-finan banza na batsa.
4. Yayin d mutum yaje cikin janaba, saboda babu garkuwa
na tsarki a jikinsa.
ALAMOMIN SAMUWAR ALJANI A JIKIN DAN ADAM.
a. Yawan mantuwa mai tsanani.
b. Mutuwar wani bangare na jiki, hannu ko kafa wanda
baya jin magani.
c. Yawan samun damuwa da kuncin rai.
d. Rashin nitsuwa a guri daya.
e. Yawan kokwanto.
f. Firgita a cikin barci.
g. Yawan mafarkin matattu.
h. Yawan mafarkin jinni ko ruwa.
i. Mafarkin maciji.
j.Jin motsi kamar ana binka a baya.
k. Cizon hakuri a cikin barci.
l. Yawan rashin bacci.
m. Yawan farkawa daga bacci.
n. Mafarkin Shanu.
o. Mafarkin saduwa ba bias ka'ida ba, kamar sau 3 fiye da
haka a sati.
p. Yawan zubar jinin haila wanda ya wuce misali.
q. Yawan zancen zuci.
r. Rashin amincewa da mutane.
s. Yawan faduwar gaba.
t. Tafiya ko tsayuwa a cikin bacci.
u. Yawan mafarkin abubuwan ban tsoro.
v. Yawan yawace yawace ba bias qa;ida ba.
w. Yawan jin tsoro haka kurum.
x. Yawan jituwa tsakanin miji da mata.
y. Jin sauti kamar ana kiranka.
z. Dadewa a bandaki ba tare da wani dalili ba.
aa. Zancen zuci a bandaki.
bb. Mafarkin kyanwa (mage). Da sauransu.
Da zaran dan Adam ya ji wannan alamomin a jikinsa, to
akwai alamar samuwar aljani a tattare das hi, sai ya fara
addu'a da yawan azkar, da yawaita karatun alku'ani.
Idan kuma ya fara jin ciwon kai, ciwon kirji, ciwon baya, ko
ciwon gabobi, bayan wadncan alamomi da suke sama, sai
ya ci gaba da addu'a tare da shan magani, in kuma abun
yayi tsanani, sai ya nemi Malamim Ruqiyya (Ahlus
Sunnah), su yi masa, karatun Alkurani. Allah ya tsare mu.
ABINDA AKE KIRA JINNUL ASHIK:-
Shi ne mace ta wayi gari tana yawan mafarki wani na
saduwa da ita cikin barci, wannan al'amarin ya kasance ya
yi yawa a tsakanin mata kuma har ya kai ga wasu
cututtuka suna faruwa ga mace ko namiji ko kuma
cututtukan da ba sa jin magani a yi ta wahala har a gaji.
DALILIN SAMUWAR JINNUL ASHIK:-
Malaman duniya sun bayar da fatawowi cikin Alqur'ani da
Sunnah, kamar cikin Majmu'ul fatawa na Shaikul Islam
ibnu Taimiyyah da littafin Ash-shifa'u bil qur'an minal jinnu
wash shayadini na Ridha Ash-sharkawi da littafin Minhajul
qur'an li'ilaj as-hir wal massi as-shaidani suka ce:
Wannan Aljani da ake kira jinnul Ashik yakan samu mace
ta hanyoyi hudu kamar haka:-
<1>: Wata shi yake kawo kansa saboda rashin kyautata
sutura da shigar banza na kayan zamani, wanda
musulunci ya hana.
. <2>: Wata kuma ita take kai kanta inda aljanun suke,
kamar zuwa wajen bokaye.
<3>: Wata kuma sihiri aka yi mata saboda ta hada nema
da wani maras tsoron Allah.
<4>: Wata kuma tana kyautata sutura, tana bin Allah,
amma Allah zai jarrabe ta da wannan shaidani.
A takaice dai wadannan hanyoyin da shi wannan shaidani
zai zo wajen ta sai ya mayar da abin ya koma zuwa
soyayya ya raba ta da kowa ya hanata yin aure ko ya
rabata da mijinta ko ya hanata zaman lafiya da shi, shi
kuma Aljanin ya ci gaba da zama da ita yana saduwa da
ita ya dauke ta kamar matarsa kuma ya hana mijinta
komai da ita, ya sa gaba da kiyayya a tsakani. Allah ya
kiyaye.
HANYOYIN DA YAKE BI YA ZO MATA A MATSAYIN MIJIN
DARE.
SUNE KAMAR HAKA:-
<1>: Yakan zo wa mace cikin barci ya dinga saduwa da ita
cikin mafarki, ta fuskar mijinta ko wani wadda take jin
kunya ko wadda bata sani ba ko dan uwanta ko ta siffar
mace 'yar uwarta.
<2>: Yakan zo mata a siffar mijinta yana saduwa da ita a
zahiri ba a mafarki ba, amma kuma shaidani ne ba mijinta
ba ne.
<3>: Yakan zo wa mace tana kwance ta ji kamar ana
saduwa da ita, ita ba mafarki ba, ita kuma ba idon ta biyu
ba.
<4>: Wata macen ta kan kwanta ta yi barci ba wadda ya
sadu da ita, amma idan ta farka ta wayi gari sai ta ga
kamar wani ya sadu da ita.
ALAMOMIN MIJIN DARE:-
Daga cikin alamomin da mace zata gane tana da wannan
matsalar shine:-
Shi wannan shaidanin zai dinga zuwa yana saduwa da ita
cikin barci, yawanci mata suna tsintar kansu cikin wannan
yanayin, amma sai su dauka shirmen mafarki ne kawai, to
a gaskiya ba haka bane. Duk mata ko budurwar da take
irin wannan mafarkin za ka same ta tana fama da
wadannan matsalolin, ko da za ka tambaye ta wadannan
matsalolin za tace maka tana fama da su. Daga ciki
akwai:-
<1>: Bacin rai ba a mata komai ba, ta ji tana jin haushin
kowa har ma da mijinta ko kuma ta ji kamar mijin ya sake
ta, ta gaji da auren, da za ka tambayeta laifin mijin ba
zata fadi laifinsa ba, wata rana ma ta ji tana tsanar
'yan'yanta.
<2>: Yawan ciwon kai daga lokaci zuwa lokaci kuma baya
jin magani.
<3>: Tsananin ciwon kirji da ciwon baya.
<4>: Tsananin ciwon mara lokacin al'ada da kuma zubar
wani ruwa daga farjin mace, shi ba al'ada ba ne, kuma ya
kasu kashi 2; mai yauki da maras yauki ko mai kauri
kamar koko tare da yawan kaikayi ko fitowar kuraje.
<5>: Ga yawan zubar ciki ko bari, ko kuma rashin samun
ciki, amma za ta iya kasancewa ta dauki alamomi na
masu ciki har ma ana zaton tana da ciki, amma ana
kwana 2 sai ta canza kamar ba ciki ba, ko ta rinka yawan
mafarki ta haihu.
<6>: Idan mijinta yana saduwa da ita tana jin zafi, ko kuma
yana saduwa da ita ba zafi, amma bata samun biyan
bukata.
<7>: Daf da magariba ta dinga jin zazzabi ko faduwar
gaba ko yawan tsorata, ko kasala da bacin rai.
<8>: Idan ta dauki Alku'ani za ta karanta sai ta dinga jin
kasala da hamma da hawaye da barci da zarar ta ajiye
kur'anin sai ta ji wartsake kamar ba ita take jin barci ba.
<9>: Sannan kuma ko ta kwanta tana son yin barci sai ta
kasa, ta yi ta juyi ta kasa barci, mijinta na zuwa kusa da
ita sai ta dinga samun firgita da tsoro.
<10>: Ko ta wayi gari gashin kanta ya dinga kadewa ko ya
yi ja, bakinta ya dinga bushewa ko yayi ja.
<11>: Yawan kaikayin ido da kaikayin kai na amosani,
amma ba amosani ba ne.
<12>: Yawan kaikayin kunne da yawan kaikayin hanci
kamar mura, amma ba mura bane, ko yawan kunburin
ciki.
<13>: Yawan zuban jini daba na al'ada ba, ko jini ya rika yi
mata wasa.
Sannan kuma har ma wacce bata da aure budurwa ko
bazawara za ta iya samun wannan matsalar, amma ita
bambancin da ke tsakanida ita wacce take da aure shine
kamar haka:-
<1>Ita marar aure za ta kasance duk lokacin da wani ya
zo wajen ta da maganar aure kamar za a yi sai abin ya
lalace daga wajen ta ko daga wajensa.
<2>Za ta dinga samun munanan mafarkai tare da ganin
wani namiji yana zuwa yana saduwa da ita cikin barci ta
fuskar da ta sani ko bakuwar fuska ko mace 'yar uwarta.
<3>Kuma za ta dinga yawan samun cututtuka masu wuyar
magani har ma da yawan zubar da jini ko ciwon mara
lokacin al'ada ko kasala lokacin karatun kur'ani, tana
farawa sai hamma da kasala ya kama ta ko kuma idan ana
sallama da ita, sai ta rinka jin faduwar gaba ko tsoro.
<4>Kuma za ta rinka yawan samun sabani da kiyayya
tsakaninta da iyayenta ko 'yan uwanta ko jama'a ko kuma
ta zama mai rashin kunya da rashin magana ga iyaye da
sauran dangi.
Allah ya kiyaye.
GAME DA NAMIJI:
Dukkan wadannan bayanai da aka yi game da 'yan uwa
mata, to sukan iya samun da namiji, amma bambanci
shine:-
Shi namiji macen Aljana ce za ta dinga zuwa wajensa ta
zama ta raba shi da kowa sai ita kadai, ta dauke shi
kamar mijinta, idan mai mata ne ta cire soyayya da
sha'awa tsakaninsa da matarsa, kuma ta hana shi komai
na ci gaban rayuwa ta mayar da shi marar kishin kansa
da rayuwarsa.
Idan saurayi ne takan hana shi karatu ko ya fara ba zai
gane ba, ko kuma inya gane ta hana shi karatun ko ta
dinga sa masa wasuwasi da kokwanto lokacin jarrabawa
ya fadi ko a kore shi a makarantar, in ya kama neman aure
ko a ki shi ko shi ya ki, in ya kama sana'a sai ya yi ta
samun matsala, kuma shi ba shan Giya, ko mata yake
nema ba, kuma tasa gaba da rashin yarda tsakaninsa da
iyayensa ko jama'a.
MAFITA:
Duk wadannan abubuwa da aka fada ba abubuwa ne
sabbi ko baki ba, ba kuma yau ko jiya aka fara samun
wannan matsalar ba, wannan matsalar an same ta tin
zamanin Annabi (SAW) game da Aljani ko Aljana ya shiga
jikin dan Adam namiji ko mace.
Imam Bukhari ya ruwaito hadisi zamanin Annabi (SAW) an
samu wata mace ta zogaban Annabi da matsalar cutar
Aljani ya kayar da ita, ta fadi, ta ce Annabi ya yi mata
magani.
Sai Annabi (SAW) y ace mata, da a bar barki dad a cutar ki
mutu ki shiga aljannah, da a yi miki addu'a ki warki, wane
ki ka fi so?! Ta cewa Annabi (SAW) idan wannan cutar za
ta zama sanadin shigata Aljannah, a barta da shi, amma
ayi mata addu'a idan ya kada ita, ta dai na tsiraici.
Don haka wannan al'amari ba bako bane ga musulmi ko
Ahlus Sunnah.
Komawa zuwa ga Allah (SWA) da kuma rike addu'o'in dad
a Manzon Allah (SAW) ya ba muna safe, yamma da na
shiga ban daki da fita, da na lokacin kwanciya, da na
sanya sutura da cirewa, da na cin abinci, duk wadannan
suna cikin littafin (HISNUL MUSLIM), sannan kuma sai
wadannan hanyoyin da Malami suka bayar guda 11, ga me
da mace ko namijin da suka samu kansu da namijin dare
ko macen dare:
1. Su kiyaye dokan Allah (SWA) da nisantar laifuka manya
da kanana.
2. Yawaita karatun Kur'ani a kawane hali a kuma kowane
lokaci.
3. Kyautata sutura (mace) hijabi, tin daga sama har kasa,
mai kauri kuma mai fadi bana adoba.
4. kiyaye cin halal wanda za a ci ko wanda za a nema.
5. Yin sallah akan lokaci tare da kiyaye ilmin sallah din tin
daga Annabi (SAW).
6. Yawan yin Alwala lokacin da za a kwanta bacci da
kowane lokaci.
7. Yawan karanta Ayatul Kursiyyu da Amanar Rasulu,
kulhuwa, Falaqi da Nasi lokacin kwanciya.
8. Yawan karanta Suratul Baqara a gida ko dakin da ake
kwana da cire hoto ko na waye.
9. Yawan Karanta:- LA'ILAHA ILLALLAHU WAHADAHU LA
SHARIKA LAHU, LAHUL MULKU WA HUWA ALA KULLI
SHAI'IN QADIR. Sau 100 da safe da yamma.
10. Karanta BISMILLAHIL LAZI LA YADHURRU MA'A
ISMIHI SHAI'UN FIL ARDHI WA LA FIS SAMA'I, WA
HUWAS SAMI'UL ALIM. Sau 3 da safe da yammaa.
11. Da Karanta: A'UZU BIKALIMATILLAHIT TAMMATI MIN
SHARRI MA KHALAK. Sau 3 safe da yamma.
HANYA TA BIYU.
Game da wadanda suka tsinci kansu cikin wannan
matsalar, ta jinnul Ashik, za ta samu tsabar habbatus
Sauda, sai ta karanta Suratul Baqara gaba daya a cikin
wannan tsabar, sai a dinga hayaki a dakin da take kwana,
kuma sai ta tsuguna kan hayakin ya dinga shiga jikinta, za
ta rinka yin haka da safe da lokacin da lokacin kwanciya.
Sai kuma amfani da magungunan Islama wadda
musulunci ya karantar ayi amfani das u
DAGA TASKAR DANDALIN AMINU YAHUZA
08080678100
Comments
Post a Comment