HANYOYIN MAGANCE FITSARIN KWANCE
*HANYOYIN WARKARDA FITSARIN KWANCE YARA DAMANYA*
🧖🏼♂🧖🏼♀🧖🏼♂🧖🏼♀🧖🏼♂🧖🏼♀🧖🏼♂🧖🏼♀🧖🏼♂🧖🏼♀🧖🏼♂🧖🏼♀
Ita wannan matsalar ana iya shawo kanta ne ta hanyoyi guda biyu kamar haka :
MAGANI : A nemi kwayoyin habbatus sauda, a rika yiwa yaro hayaki dasu. Kuma yana dan tsugunawa akan hayakin. Sannan kuma a rika gauraya masa habbatus sauda din yana shan cokali guda tare da zuma. Ko kuma ya shafe jikinsa da man Habbatus sauda din wanda akayi tofi acikinsa. In sha Allahu zai dena.
2. ADDU’A : Arika tofa masa wannan addu’ar, ko kuma akoya masa ya rika yinta da kansa, ko kuma a rubuta masa ajikin takarda ya sanya ajikinsa yayin da zai kwanta.
Kamar yadda aka ruwaito daga Abdullahi bn Amru bn Al-As Sahabin Manzon Allah (saww) yana rataya ma ‘ya’yansa Qanana wannan addu’ar. Gata nan kamar haka :
“ ﺃﻋﻮﺫ ﺑﻜﻠﻤﺎﺕ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺘﺎﻣﺎﺕ ﻣﻦ ﻏﻀﺒﻪ ﻭﻋﻘﺎﺑﻪ ﻭﻣﻦ ﺷﺮ ﻋﺒﺎﺩﻩ ﻭ ﻣﻦ ﻫﻤﺰﺍﺕ ﺍﻟﺸﻴﺎﻃﻴﻦ ﻭ ﺃﻥ ﻳﺤﻀﺮﻭﻥ ”.
‘A’udhu bi kalimatil Laahit tammati min ghadhabihee wa ‘iqabihee wa min sharri ibadihee wa min hamazatish shayateen wa an yahdhurooni.
FASSARA : Ina neman tsari da cikakkun kalmomin nan na Allah daga fushinsa da Uqubarsa, kuma daga sharrin bayinsa, kuma daga sharrin fizge-fizgen shaitanu, kuma (ina neman tsarinsa) kada su halartoni.
In sha Allahu koda babban mutum ne yake fama da matsalar fitsarin kwance, in dai ya lazimci wadannan abubuwan tare da gaskatawa zai ga biyan bukatarsa.
*DAGA MATSALOLIN MA'AURATA GROUP*
08080678100
Assalamu alaikum nidai Ina da Diya shekararta Sha takwas ammahar yanzubata dainaba anatamagani Allah yataika adace.
ReplyDelete