*ABUBUWA GOMA DAKE HANA MATA JIN DADIN JIMA'I* ✍🏻 1. CIWON SANYIN MARA KO MATSALOLIN MARA DA MAHAIFA: Kama daga sanyin mara (vaginities/toilet infections, UTI & STDs), yoyon fitsari, 'kululun mahaifa (fibroid), da sauran cututtukan al'aura na daga cikin abubuwan da ka iya hana mace jin dadin jima'i.Misali, sanyin gaba mai zuwa da 'yan 'kananan kuraje cikin farji , na sanya mace taji zafi wajen jima'i yayinda zakari ke kai-kawo cikin farji, wanda sau da yawa masu kurajen basu ma san suna da kurajen ba cikin al'aura, saidai suce suna jin zafi lokacin saduwa. Kurajen suna fashewa saboda da gugar zakari, sai wurin ya zama rauni. Hakan nasa mata tsoron jima'i da ganinsa abin azabtarwa gare su mai maimakon abin jin dadi. Sau tari basu san abinda ya haddasa zafin ba, wanda kuma mai yiwuwa ciwon sanyi. Ciwon sanyi na iya dakushe sha'awar mace ko namiji. Ciwon sanyi na iya haddasa bushewar gaba (vaginal dryness) wanda alamunsa shine daukewar ni...